Za mu kare kanmu da karfin makamai — Korea ta Arewa

Korea ta Arewa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Korea ta Arewar ta ce za ta kare kanta da karfin makaman da take da su

Koriya ta Arewa ta mayar da martani ga wani yunƙurin Amurka na aika jirgin dakon jiragen yaƙi zuwa yankunan gaɓar tekun Koriya, ta ce za ta kare kanta da wani gagarumin ƙarfi na makamai.

Kamfanin dillancin labaran gwamnatin Koriya ta Arewa ya ruwaito ma'aikatar harkokin wajen ƙasar na cewa, halin da aka shiga wata shaida ce da ke nuna gaskiyar ƙasar na ɗaura wa kanta ɗamara ta kowacce hanya ciki har da makaman nukiliya.

Ministan harkokin wajen kasar ya ce aikewa da jiragen yakin, kutse ne na ganganci, da ya kai makura.

Rundunar sojin Amurka ta yankin Pacific ta ce tana da burin zama cikin shiri a yankin tekun Koriya.

Shugaba Donald Trump ya ce Amurka a shirye take ta dauki mataki ita kadai wajen dakile duk wata barazana kan makaman nikiliya daga Korea ta Arewar.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Korea ta Arewar ta sha yin gwaje-gwaje makaman nukiliya

Korea ta arewa ta gudanar da gwaje-gwaje da dama na makamai masu linzami.

Ta ce atisayen sojoji tsakanin Amurka da Korea ta Kudu ne ke sanya zama cikin shiri don kawar da duk wani yunƙurin yi mata yi mata kutse.

A ranar Lahadi, jami'an tsaron Amurka sun ce an umarci wata zugar sojan ruwa mai kai farmaki , da ta ƙunshi jirgin ruwan dakon jiragen yaƙi, da wasu jirage masu tarwatsa makamai masu linzami sun nausa zuwa yankin Koriya.