Amurka ta yi wa Syria ɓarna da sunan ramuwa

Syria

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Harin iska mai guba da ake zargin kasar Syria da kai wa a garin Khan Sheikhoun a makon jiya ya hallaka mutane 89 da jikkata da dama

Amurka ta ce ta lalata kashi 20 cikin 100 na jiragen sojan Syria a wani harin makami mai linzami da ta kai cikin makon jiya, a matsayin ramuwa kan wani hari da ake gani na iskar gas ne.

Sakataren tsaron Amurka, James Mattis ya ce harin ya nakasa ƙarfin gwamnatin Syria na zuba wa jiragenta mai da ɗaura musu makamai a sansanin jirgin sama na Shayrat.

Mai magana da yawun fadar White House Sean Spicer ya ce, duk wani harin makamai masu guba ko bama-baman mai daga gwamnatin Syria a nan gaba ka iya fuskantar tirjiya daga sojan Amurka.

Syria dai ta musanta kai harin iska gas mai guba a kan garin Khan Sheikhoun da ke karkashin ikon 'yan tawaye, abin da ya yi sanadin asarar rayukan mutane 89 tare da jikkata da dama.

Bayanan hoto,

Shugabannin Amurka da Burtaniya na ƙoƙarin jan hankalin Russia don ta dawo daga rakiyar shugaba Assad.

Sakataren harkokin tsaron Amurka Jamed Mattis ya ce harin ya haifar da lalacewar wuraren ajiye makamai da man jiragen yaƙi, har ma yanayin tsaron sararin samaniya.

Mr Mattis ya ce farmakin ya nuna cewa Amurka ba za ta tsaya ta zuba ido tana ganin shugaba Bashar-al-assad na hallaka mutane da iska mai guba ba.

Shugabannin Amurka da Burtaniya sun ce akwai sauran damar da za a ja hankalin Rasha don ta dawo daga rakiyar shugaba Bashar al-Assad.

Ministocin harkokin waje daga kasashe 7 masu karfin arzikin masana'antu na wata ganawa ta kwanaki biyu a kasar Italiya, don cim ma matsaya guda a kan Syria.

Sakataren harkokin wajen Burtaniya Boris Johnson, ya ce suna tunanin kara aza Rasha takunkumi da kuma jami'an sojin kasar Syria.