Uba ya harbe ɗansa saboda gardama a kan kare

Chicago shooting

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wata jaridar yankin ta ce an harbi mutum sama da 800 a bana kaɗai ya zuwa yanzu

Wani mutumin Chicago ya bindige ɗansa mai shekara 22, bayan gardama ta barke tsakaninsu a kan wanda ya kamata ya raka kare tattaki, lamarin da har ya kai su ga musayar harbe-habe.

'Yan sanda sun ce mutanen sun zaro bindigogi yayin hayaniyar da ta barke a unguwar Burnside ranar Lahadi, ko da yake ba su yi ƙarin bayani ba.

Uba da ɗan sun yi wa kansu jina-jina, lamarin da ya sa aka garzaya da su asibiti, a can ne kuma aka ba da sanarwar mutuwar ɗan.

Turawa sun yi suna wajen fita da karnukansu zuwa tattaki, a wani yunƙuri na sanya su motsa jiki ta yadda goɓoɓinsu za su ware.

Hukumomi sun ce shi kansa uban mai shekara 43 yana cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai.

Wani mai magana da yawun 'yan sandan Chicago, Anthony Guglielmi ya tabbatar da faruwar harbe-harben.

'Yan sanda sun gano makami biyu a wurin da lamarin ya faru kuma tuni har sun fara bincike.

Jaridar Chicago Tribune ta ce Chicago na ɗaya daga cikin biranen Amurka mafi fama da tarzoma, inda ya zuwa yanzu aka harbi mutum sama da 800 a bana kadai.