Ɗalibai sun yi arangama da 'yan sanda a Niamey

Jamhuriyar Nijar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Daliban Nijar na zanga-zanga a Yamai babban birnin kasar kan tabarbarewar harkar karatunsu

An kama gomman ɗalibai da suka gudanar da wata zanga-zanga a Niamey babban birnin jamhuriyar Nijar, bayan sun yi arangama da 'yan sanda.

Ɗaliban sun riƙa jifa da duwatsu yayin da 'yan sanda suka harba hayaƙi mai sa hawaye.

Shugabannin ɗaliban sun ce an kashe ɗalibi guda, yayin da wasu da dama suka jikkata, sai dai babu tabbaci daga hukumomi a kan batun mutuwa da jikkatar ɗaliban.

Ɗaliban dai sun gudanar da zanga-zanga ne don nuna adawa kan mummunan halin rayuwa da na karatunsu, haka kuma sun ce ba a ba su tallafin karatu ba tsawon wani lokaci.

Haka zalika, an samu makamanciyar wannan zanga-zanga a biranen Maraɗi da Zinder.