An ci zarafin wani fasinja a cikin jirgi a Amurka

Bayanan bidiyo,

Bidiyon yadda abin ya faru

Shugaban kamfanin jirgin sama na United Airlines ya ce ma'aikatansa sun bi ka'idojin da aka tsara ne, a yayin wani lamari da ya afku da ya kai ga fitar da wani fasinja da karfi daga cikin jirgin.

A wata wasika da ya rubutawa ma'aikatan, Oscar Munoz ya ce ransa ya yi matukar baci da ya ji abin da ya faru.

Amma kuma ya kara da cewa, fasinjan ne ke da laifi, domin ya nuna turjiya.

Tun da farko kamfanin jirgin saman, ya ce zai gudanar da bincike kan lamarin, bayan da wani bidiyon da ya nuna yadda ake jan fasinjan a kasa ya janyo cece-ku ce a shafukan sa da zumunta.

Hoton bidiyon da aka nada daga cikin jirgin, ya nuna yadda aka dinga jan mutumin tun daga kujerarsa a cikin jirgin a kasa har aka fitar da shi.

Daga baya kuma aka nuno shi duk jina-jina da jini a fuskarsa.

Ba a tabbatar da sunan mutumin ba, amma wani fasinja da ke zaune kusa da shi ya shaida wa BBC cewa, dan asalin kasar Vietnam ne, da ya kwashe shekara 20 yana zaune a Louisville Kentucky da ke Amurka.

A yammacin ranar Lahadi ne jirgin wanda ya taso daga Chicago a kan hanyarsa ta zuwa Louisville, ya sayar da tikitin da yawan su ya fi kujerun cikin jirgin.

Ma'aikatan jirgin sun bukaci fasinjoji hudu su sauka daga cikin jirgin, saboda ma'aikatansu hudu su samu wuri.

Mista Munoz dai ya sha suka a shafukan sada zumunta, sakamakon martanin da ya mayar kan lamarin.

Duk da cewa a wasikar da ya rubuta wa ma'aikatan jirgin, ya ce ransa ya yi matukar baci da jin abin da ya faru, amma kuma ya kare abin da ma'aikatan suka yi.

Mista Munoz ya ce fasinjan ya nuna turjiya ne da aka bukace shi da ya sauka, don haka babu yadda ma'aikatan suka iya face su tursasa masa ficewa daga cikin jirgin, inda dole sai da aka hada da jami'an tsaron jiragen sama.

Asalin hoton, Jayse D Anspach

Bayanan hoto,

Ba a tabbatar da sunan Fasinjan ba, amma ya shaida wa abokan tafiyarsa cewa shi Likita ne

Asalin hoton, Tyler Bridges/Twitter

Bayanan hoto,

Jami'an tsaron jiragen sama ne suka fitar da shi da karfi daga cikin jirgin

Akwai rahotannin da ke cewa mutumin dan asalin China ne kuma mazaunin Amurka, a don haka ne kuma shafukan sada zumuntar China suka kaure da nasu ce-ce-ku-cen.

Asalin hoton, Twitter

Asalin hoton, Twitter

Jayse D Anspach ne ya sanya hoton bidiyon abin da ya faru cikin jirgin, kuma ya wallafa a shafinsa na Twitter, inda ya ce, "#United ta karbi kudin fasinjoji fiye da kima, kuma ta bukaci hudu daga cikin mu da su bayar da hadin kai su sauka, saboda ma'aikatansu da za su shigo domin aiki washe gari."

Ya kara da cewa, "Babu wanda ya bayar da hadin kai, sai kawai suka yanke shawarar cewa wani Likita dan Asiya da matarsa da su sauka."

"Likitan ya ce yana da aiki a asibiti washe gari, don haka ya ce shi ba zai sauka ba, don haka suka masa ta karfi. Bayan mintuna goma sai ya rugo ya dawo, ga kuma jini a baki, yana sumbatu yana cewa 'ina bukatar in je gida'." In ji Mista Anspach.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Shugaban kamfanin jiragen sama na United Airlines Oscar Munoz yana sha kakkausar suka

Sashen kula da harkokin jiragen sama a jihar Chicago ya ce an tura daya daga cikin jami'an da ke da hannu a ciki zuwa hutun dole, saboda a cewar su ba za su dauki irin wannan hali ba, amma za a gudanar da sahihin bincike.

Simon Calder dai dan jarida ne kuma masanin harkokin tafiye-tafiye, ya kuma ce matukin jirgi na da ikon ya fidda duk wanda ya ke so daga cikin jirgi.

Duk wanda ya nuna turjiya kuma za a iya fidda shi da karfi, saboda ya yi biris da umurnin matukin jirgin.