'Da gangan aka kai wa Borussia Dortmund hari'

Motar tawagar kwallon kafa ta Borussia Dortmund

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Gilasan tagogin da tayoyin motar sun farfashe a tashin bam din

Yan sanda a Jamus sun ce da gangan aka kai hari abubuwa masu fashewa kan motar bus ɗin da ke dauke da 'yan kwallon kafa na Borussia Dortmund a wajen otal din da suka sauka.

An far wa motar ce da abin fashewa uku, lokacin tana kan hanyarta ta zuwa filin wasan Dortmund, gabanin wasan cin kofin Zakarun Turai da za su buga da Monaco.

A wani taron manema labarai, wata jami'ar bincike a Jamus ta ce ana gudanar da bincike kan wata wasiƙa da aka samu a kusa da inda aka kai harin, amma ba ta bayar da cikakkun bayanai ba.

Mahukunta sun yi kashedi game a kan yaɗa jita-jita, da kuma saurin danganta lamarin da harin ta'addanci .

'Yan sandan Jamus sun ce abubuwan fashewa uku ne suka fasa tagogin motar, kuma har ɗan wasan ƙungiyar ɗaya ya ci rauni.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Dan wasan baya na Borussia Dortmund dan kasar Spaniya Marc Bartra ya samu rauni

Tuni aka yi wa ɗan wasan bayan Dortmond dan kasar Spaniya-- Marc Bartra -- tiyata, bayan raunin da ya samu a hannu daga gilasan motar da suka farfashe.

Wani ɗan jarida Sebastian Kolsberger ya faɗa wa BBC cewa ya je masaukin 'yan wasan jim kaɗan da komawarsu bayan aukuwar harin.

Kamfanin dillancin labarai na Jamus ya ce mahukunta na gudanar da bincike kan abubuwa da dama da ka iya zama musabbin kai harin.

Haka kuma, za a girke jami'an tsaro da dama a wasan da Dortmund ɗin za ta buga a Larabar nan, bayan an ɗage shi daga Talata.

Kulob din Dortmund dai ya buƙaci magoya bayansa su kwantar da hankula.