Mun fi fama da almajirai daga jihar Katsina - Kano

Kananan yara a Nijeriya
Bayanan hoto,

Kananan yara sama da miliyan ɗaya ne ke gararamba a kan titunan arewacin Nijeriya

Ƙididdiga ta nuna cewa ƙananan yara fiye da miliyan ɗaya ne a Nijeriya ba sa zuwa makaranta, kuma akasarinsu na yawon barace-barace a tituna.

Yawon bara a tsakanin ƙananan yara na daga cikin manyan ƙalubale da ke addabar arewacin Nijeriya, kuma lamarin ya ƙi jin magani duk da illar hakan a tsakanin al'umma.

Wasu jihohin ƙasar kamar Kano sun yi dokokin hana bara da suka tanadi kama almajiri da malaminsa, amma har yanzu matsalar ba ta ragu ba maimakon haka ma ƙara gaba-gaba take yi.

An ware yau Laraba 14 ga watan Afrilu a matsayin ranar tunawa da yaran da ke gararamba a kan tituna a sassan duniya.

A Nijeriya dai, an fi samun gararambar yara a tituna da sigar bara, inda dubban ɗaruruwan yara ke shafe tsawon wuni suna yawo don neman abinci.

Bayanan hoto,

Ƙananan yara almajirai kan fada hadurra da dama a lokacin da suke yawon bara

Yaran dai ba sa zuwa makarantun boko don haka babu abin da suka iya a rayuwa sai bara, kuma kalmar da suka fi riƙe wa a baki ita ce "a taimaka mana da abinci."

Sau da dama almajiran na faɗa wa haɗurran rayuwa iri daban-daban, kamar yadda wani ƙanƙanin yaro ɗan kimanin shekara takwas da ya ɓata a wajen yawon bara a Kano.

Yaron wanda aka kai shi Kano almajiranci ya ce sunan ƙauyensu Daburam amma bai san a cikin jihar da yake ba, ya shafe sama da mako ɗaya yana kwana a titi.

Ya ce ''Makaranta aka kawo ni, ina zuwa yawon bara, lokacin da na ɓata bana kwana a makaranta, a wani budadden wuri nake kwana, ina shimfida leda sai in kwanta.''

Irin wadannan matsaloli ne dai suka sa gwamnatin jihar Kano ta haramta barace-barace, kuma tun bayan fara aikin wannan doka, an kama dubban almajirai da suke kunnen kashi.

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa shi ne kwamandan Hizba da ke kamen masu barar ya ce "Kananan yaran (da suka kama ya zuwa yanzu) sun kai dubu biyar da talatin da biyar da dari shida.

"Galibi sun kwararo ne daga jihohi Nijeriyar kusan 16, jihar Katsina (daga) nan muka fi samun yara almajirai da yawa''

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Hukumar Hizbah ta Kano ta ce matsalar barace-barace a tsakanin ƙananan yara ta-ƙi-ci-taƙi-cinyewa

A cewar darakta Janar na hukumar ta Hizbah Malam Abba Sa'id Sufi suna bin matakai daban-daban idan sun kama masu barar.

An dai sha gudanar da bincike da nazarce-nazarce da dama gami da ba da shawarwari kan yadda za a magance matsalar bara, musamman a arewa.

Cikin aikace-aikacen har da na wani kwamitin wasu fitattun mutane da suka shafe wata takwas suna yi wa gwamnonin arewa nazari kan wasu matsaloli musamman na bara, sannan suka gabatar da rahoto yadda za a magance su.

Sai dai sama da shekara uku da mika wa gwamnonin wannan rahoto har yau babu ko shawara ɗaya da suka fara aiwatarwa.