Ana sayar da 'yan ci-rani a 'kasuwar bayi' ta Libya

Migrants

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ana la'akari da ƙwarewar sana'ar da ɗan ci-rani yake da ita wajen yi masa farashi a yayin sayarwa

Hukumar kula da ƙaura ta duniya ta ce ana sayar da 'yan Afirka da ke tafiya ci-rani zuwa Turai a "kasuwannin bayi" da ke cikin Libya.

Waɗanda abin ya ritsa da su sun faɗa wa hukumar kula da ƙaura cewa bayan masu fasa-ƙwaurin bil'adama ko ƙungiyoyin sojan sa-kai sun tsare su, sai a ɗauke zuwa dandali ko tasha don sayarwa.

Ana sayar da 'yan ci-rani masu ƙwarewar sana'o'i kamar fenti ko shimfiɗa tayel, da tsada a cewar shugaban hukumar a Libya.

Libya ta shiga hargitsi tun bayan hamɓararwar da mayaƙa masu goyon Nato ta yi wa Muammar Gaddafi a shekara ta 2011.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

A cewar rahoton hukumar kula da ƙaura ta duniya ana takura wa 'yan ci-rani da yunwa da azabtarwa

Ɗaruruwan matasa daga kudu da Sahara ne ke samun kawunansu a kasuwar da ake cewa ta bayi ce a cewar rahoton hukumar kula da masu ƙaura.

'Ana tursasa wa 'yan ci-rani zama da yunwa'

Wani ɗan ci-ranin Senegal da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce an sayar da shi a ɗaya daga cikin irin wannan kasuwa da ke birnin Sabha na kudancin Libya, kafin a kai shi zuwa wani gidan yarin wucin gadi inda ake tsare da takwarorinsa sama da 100.

Ya ce akan ce wa 'yan ci-ranin da ake tsare da su a can su kirawo danginsu, waɗanda za a buƙaci su biya kuɗi kafin a sake su, har ma akan doki wasu a lokacin da auke magana ta waya don danginsu su ji yadda ake azabtar da su.

Ya bayyana 'mawuyacin' yanayin da ake tursasa wa 'yan ci-rani rayuwa ta hanyar ba su abinci kaɗan, waɗanda kuma danginsu ba su biya kuɗin da aka nema ba ana iya kashe su ko kuma a bar su cikin yunwa.

Shi ma wani shaida wanda ya iya haɗa kuɗin da nema kafin a sake shi bayan tsawon wata tara, daga bisani sai da aka kai asibiti saboda yunwa ya rame ƙarƙaf.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Akasarin 'yan ci-ranin na kan hanyarsu ne ta tsallaka teku zuwa nahiyar Turai

Bayanan hoto,

Wasu daga cikin 'yan ci-ranin na fitowa ne daga yankin Afirka ta yamma

Ya ce su ma mata, ana sayar da su ga fararen hula 'yan Libya waɗanda suke kai su gidajensu don yin lalata da su.

Shugaban hukumar kula da ƙaura a Libya, Othman Belbeisi ya faɗa wa BBC cewa ana yi wa 'yan ci-ranin kuɗi ne daidai da ƙwazonsu.

Wani jami'in hukumar kula da ƙaura a Nijar ya ce sun tabbatar da rahotannin gwanjon da ake yi wa 'yan ci-rani a Libya daga bakin waɗanda suka kuɓuta.

"Duka sun tabbatar da kasadar cewa ana iya sayar da mutum a matsayin bawa, ko dai daga direbobi ko kuma 'yan gari waɗanda suke ɗaukar 'yan ci-rani musammam aikin gini a garin Sabha.

"Daga baya, maimakon su biya su haƙƙinsu, a'a, sai su sayar da su ga sabbin masu buƙata."

Wasu 'yan ci-ranin, akasari 'yan Nijeriya da 'yan Ghana da 'yan Gambia ana tursasa musu yin aiki "a matsayin 'yan gadi a gidajen da ake tsare takwarorinsu ko kuma a 'kasuwar' kanta", in ji wani ma'aikacin hukumar kula da masu ƙaura.