An tuhumi matar da ta yi wa ɗan tasi fyaɗe

Brittany Carter

Asalin hoton, HANCOCK COUNTY JAIL

Bayanan hoto,

Abokin matashiya Brittany Carter a lokacin aikata wannan laifin ya tsere

An tuhumi wata matashiya daga jihar Ohio a Amurka da zargin yi wa wani direban tasi fyaɗe.

'Yan sanda sun ce daga bisani kuma sai Brittany Carter da wani mutum suka yi wa dan tasin fashi a yankin Findlay.

An zargi Brittany, mai shekara 23 da yin lalata da direban mai shekara 29, yayin da wani matashi, Corey Jackson da suke tare mai shekara 20, ya sa wa direban wuƙa a wuya.

Daga nan kuma sai suka ɗauke masa dala 32 kafin su tsere.

Wani jami'in 'yan sanda, Laftanal Robert Ring ya ce "Ba mu san dalilin da yasa ta yi hakan ba."

"Mai yiwuwa suna so su ɗauke hankalinsa ne, saboda sun yi masa sata."

A cewar 'yan sanda lamarin ya faru ne bayan Brittany ta kira mai tasin daga Trinity Express Cab da sanyin safiyar ranar 28 ga watan Janairu.

An kama matashiyar bayan ɗan tasin ya kai rahoton fyaɗen da aka yi masa.

Yanzu dai, Brittany na fuskantar babbar tuhumar aikata fyaɗe da kuma aikata fashi a wata kotu da ke yankin Hancock.

Sau biyu ana samunta da laifi kan tu'ammali da ƙwaya a shekarar 2016 kuma an taɓa zarginta da mallakar hodar iblis.