An yi arangama tsakanin soji da 'yan sanda a Yobe

Jihar ta Yobe ta sha fama da matsalar hare-haren kungiyar Boko Haram

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jihar ta Yobe ta sha fama da matsalar hare-haren kungiyar Boko Haram.

Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da mutuwar jami'an soji biyu da 'yan sanda biyu bayan wata arangama da aka yi tsakanin bangarorin biyu a birnin Damaturu da ke jihar Yobe.

Ba a tabbatar da abin da ya haddasa rashin jituwa tsakanin jami'an tsaron ba, sai dai wasu sun tabbatar wa BBC cewa wani kwamandan 'yan sanda, CSP Dauda Buba Fika ya samu raunuka sakamakon harbin bindiga da ya same shi.

Ganau sun shaida wa BBC cewa an kai gawarwakin jami'an tsaron dakin ajiye gawarwaki na asibitin Damaturu Specialist Hospital.

Sojoji da 'yan sanda dai sun sha samun rashin jituwa a tsakaninsu, musamman a birnin Lagos da ke kudu maso yammacin kasar, lamarin da kan yi sanadiyar mutuwa da jikkata.

Jihar ta Yobe dai ta sha fama da matsalar hare-haren kungiyar Boko Haram.