Mutumin da aka wulakanta a jirgi ya shigar da kara

David Dao ke nan lokacin da ake fitar da shi daga jirgi da karfin tuwo

Asalin hoton, Image copyrightTYLER BRIDGES/TWITTER

Bayanan hoto,

Jami'an jirgin sun ce David Dao ya yi gardama ne lokacin da ake fitar da shi

Lauyoyin David Dao, wani fasinja wanda aka fitar da shi da karfin tuwo daga cikin jirgin sama na Untied Airlines ya shigar da kara a gaban koto da ke Amurka.

Fasinjan ya bukaci kotun da ke jihar Illinois ta sanya kamfanin jirgin saman da hukumomin birnin Chicago su adana duk wani bidiyo da muryoyin da aka nada na inda matukan jirgin ke zama da na fasinjoji da kuma duk wasu abubuwa da suka danganci jirgin.

An nadi bidiyon David Dao a lokacin da ake jansa a kasa jina-jina kuma yana ihu daga cikin jirgin da ya shiga a filin jirgin sama na O'hare da ke Chicago.

Kamfanin United Airlines ya ce zai mai da wa mutanen da suka hau jirgin a ranar Lahadi kudin jirgin da suka biya.

Shugaban kamfanin, Oscar Munoz, ya dage kan cewa ba zai yi murabus ba.

Kwana biyu bayan aukuwar lamarin, Dakta Dao ya ci gaba da samun kulawa a wani asibiti da ke Chicago, a cewar lauyansa kuma ana sa ran wani daga cikin daginshi zai yi jawabi a wurin wani taron manema labarai a ranar Alhamis.

Birnin Chicago ne ke kula da filin jirgin saman O'Hare.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Kamfin jirgin saman ya yi "Tayin diyya" ga fasinjojin da suka shiga jirgin saman mai lamba 3411.

A ranar Laraba ne Mista Munoz ya ce ya ji kunya sakamakon abin da ya faru ya kuma sha alwashin cewa hakan ba zai sake faruwa ba.

Da farko dai Mista Munoz ya bayyana Dakta Dao a matsayin " Mutum ne mai gardama kuma mai cike da fushi".

Amma kuma da aka tambaye shi, sai ya ce: "An dauke ni aiki ne domin na gyara al'amuran kamfanin United kuma abin da muke yi ke nan kuma abin da za mu cigaba da gudanarwa kenan".

A yammacin ranar Lahidin da ya gabata ne dai aka fitar da Dakta Dao ta karfi daga cikin jirgin saman da aka sayar wa da tikiti fiye da yadda ya kamata kuma kamfanin ya bukaci ya rage mutum hudu su bar jirgin domin su sama wa ma'aikatan cikin jirgin wurin zama.

An dai yi wa Dakta Dao jina-jina bayan jami'an tsaron sun jawo shi daga cikin jirgin a yayin da ya ki fita daga jirgin wanda zai tashi zuwa Louisville da ke Kentucky.

Bidiyon lamarin ya tayar da hankulan mutane daga sassan duniya daban-daban kuma dangin Dao sun fitar da sanarwa inda suka nuna matukar jin dadinsu saboda goyon bayan da suka samu.