Sahihan bayanai biyar da suka kamata ku sani

Yara da ke gararamba a titi

Asalin hoton, Uriel Sinai

Bayanan hoto,

Yaran da ke yawo a tituna na fuskantar barazana iri-iri

Meye ke sanya yara ragaita?

* Wasu yara a Afirka na ragaita a titi ne saboda gujewa cin zarafi a gida.

* Wasu yaran na gudun matsanancin talaucin da iyayensu ke fama da shi, sai su koma biranen domin neman mafita.

* Rasuwar iyayen yaran ma ka iya shigar da yaran cikin wani mummunan hali.

Asalin hoton, PIUS UTOMI EKPEI

Bayanan hoto,

Yakin basasa da annobar cutar AIDS na cikin dalilan da suka sa yara ke kara yawa a gari

Meye ke haddasa wannan matsalar da take shafar al'umma?

* Annobar cutar AIDS da yakin basasar da aka yi fama da shi sun yi sanadiyyar watsewar yara.

* Koma bayan tattalin arziki da rashin kyakkyawar kular gwamnatoci sun ta'azzara lamarin.

* Wasu gidan marayu na fitar da yara har 'yan shekaru 13, saboda rage cunkoso.

Asalin hoton, Michael YASSUKOVICH

Bayanan hoto,

Yaran na fama da rashin abinci da wajen kwana

Amfani da miyagun kwayoyi

* Kwayar da ya fi farin jini shi ne 'glue'. Ga shi da arha ga kuma saurin samu.

* Idan yara suka shaki 'glue', sai su shiga yanayin maye, ba za su ji matsin sanyi ko yunwa ba.

Asalin hoton, TONY KARUMBA

Bayanan hoto,

Kanana yara da manyan na shiga shan kwayoyi domin rage radadin yunwa da sanyi

Barazanar da suke fuskanta

* Duk inda suka samu wuri suke kwanciya, kuma yawanci suna shiga cikin hadari.

* Za su iya fuskantar tsangwamar 'yan sanda cikin dare, da ke karbar kudi hannunsu, da kuma barazanar manya da ke yin lalata da manya da kananan yara da ke kwana a waje.

Ayyuka da neman ilimi

* Wasu yara da ke gararamba a kan titi na zuwa makaranta, amma mafi yawan lokuta ba sa zama a aji, sakamakon haka kuma ba sa yin nasara a jarrabawa, domin rashin mayar da hankali.

* Duk aikin da yaron da ke kwana waje ke yi, zai dogara ne a kan inda ya fi zama, da kuma aikin da ke kasa.

* Ayyukan sun hada ne da sayar da kayan gwangwani ko yin rakiya ga baki masu yawon bude ido, ko kuma bara da aikin karuwanci da ake tilasta masu shiga.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Suna shiga bara domin samun abinci