Wasannin da za a yi a Gasar Firimiya

Manchseter City da Chelsea za su barje gumi
Bayanan hoto,

Manchester City da Chelsea za su barje gumi

Kulob-kulob da ke wasa a Gasar Firimiya za su ci gaba da wasa a mako na 33, inda za a yi wasanni guda 10 daga ranar Asabar zuwa Litinin.

Tottenham, wadda take ta biyu a tebur, ita ce za ta fara wasa da Bournemouth. Kodayake, ana sa ran gwarzon dan wasansu Harry Kane fara wasa tun daga farko bayan ya dawo daga rauni.

A ranar Lahadi ne za a kece raini tsakanin Manchester City da kuma Chelsea wadda take ta daya a teburi.

Ana sa ran mai tsaron gidan Manchester United David de Gea zai dawo wasa bayan raunin da ya ji a wasansu da Sunderland.

Hakazalika, 'yan wasa kamarsu Wayne Rooney da Ashley Young duka sun dawo daga jinyar rauni.

Har ila yau, Arsenal tana fuskantar kalubale bayan rashin nasarar da ta yi a makon jiya, inda Crystal Palace ta yi musu ci 3-0.

Sai dai sai a ranar Litinin ne za ta buga wasa da Middlesbrough.