Nigeria: 'Akwai gyara a kudurin dokar ilimi kyauta a Sokoto'

Gwamnatin jihar Sokoto ta ce wajibi ne iyaye su sanya 'ya'yansu makaranta
Bayanan hoto,

Gwamnatin jihar Sokoto ta ce wajibi ne iyaye su sanya 'ya'yansu makaranta

Iyayen yara a Najeriya sun fara tofa albarkacin bakinsu kan wani kudurin doka da majalisar dokokin jihar Sokoto ta amince da shi wanda zai wajabta ilmantar da kowanne yaro kyauta har zuwa shekaru goma sha takwas.

Wannan kudurin dai ya yi kama da wanda tsohon shugaban Amurka George W. Bush ya rattabawa hannu a shekara ta 2002, wanda ya wajabta wa kowadanne iyaye sanya yaransu a makaranta.

A karkashin kudurin dai, za a bawa yara daga tsakanin shekara shida zuwa goma sha takwas ilimi kyauta.

To sai dai wasu iyayen yaran sun ce ko shakka ba bu wannan mataki ne mai kyau da gwamnatin jihar ta bullo da shi, amma fa sai an yi gyara a wasu bangaren kafin a samu nasara.

Iyayen yaran sun ce, dole a samar da malamai kwararru da kuma kayan aiki a makarantun, idan har ana so a samu nasara a kan wannan kudiri.

Yanzu dai dole ne iyaye su tabbatar da cewa 'ya'yansu sun samu ilimi tun daga Firamare zuwa matakin babbar sakadire.

Jihar Sokoto dai na daga cikin jihohin Najeriya da aka bari a baya a bangaren ilmin boko, kuma tun a shekara ta 2015, mahukuntar jihar suka ayyana kafa dokar ta baci a fannin ilmin.