North Korea na baje kolin makamai

Kakansa, Kim II-sun ne ya kafa kasar
Bayanan hoto,

Kim Jong-un ya gaji mahaifinsa

Shugaban Korea ta Arewa, Kim Jong-un na duba yadda sojojin kasar suke faretin tunawa da ranar haihuwar kakansa, Kim II-sung wanda kuma shi ne ya kafa kasar.

Daya daga cikin makaman da aka baje kolinsu a wurin faretin shi ne wani sabon salon makami mai linzami da ke tafiya a karkashin ruwa.

Wannan fareti dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake musayar yawu kan gwaje-gwajen makamai masu linzami da Korea ta Arewar ke yi.

A ranar Asabar din da ta gabata ne Korea ta Arewar ta nemi Amurka ta dai na yi mata katsalanda.

A makon da ya gabata ne dai shugaban Amurka, Donald Trump ya aike da tawagar sojoji da kayan yaki zuwa Koriya ta Arewar.

Ya ce ya yi hakan ne da nufin dakile sabon yunkurin sake yin gwajin makamin mai linzami.

Mista Trump ya kuma ya nemi China wadda makwabciyar kasar ce da ta ja kunnen Koriyar.

Duk da cewa Chinar ta dan yi nawa wajen daukar mataki kan Koriya ta Arewa amma daga bisani ta hana zurga-zurgar jirage tsakaninta da Korea ta Arewar.

Rahotanni na cewa Koriya ta Arewa na dab da cimma kera wani makamin mai linzami mai dogon zango da zai iya tankarar da Amurka.

Bayanan hoto,

Wasu daga cikin irin makaman da Koriya ta yi gwaji