Kwale-kwale ya kife da mutum 150 a Kebbi

Image caption Ana yawan samun mutuwar mutane ta hanyar ruwa a Kebbi

Ana can ana ta faman aikin ceto a jihar Kebbin Najeriya, bayan da wani jirgin kwale-kwale dauke mutane kimanin 150 ya kife, a wani kogi da yammacin jiya Juma'a.

Mutanen dai 'yan kasuwa ne da ke kan hanyarsu ta dawowa daga cin kasuwa a makwabciyar jihar Neja.

Daya daga cikin mutanen da suka tsira, Muhammadu Maikuma ya ce an ceto akalla mutane 120.

Ga dai abin da ya shaida wa Haruna Tangaza ta wayar tarho:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Yadda hadarin ya faru

Labarai masu alaka