Amurka ta yi kutse a bankunan kasashen duniya

Hukumar tsaron Amurka na shan suka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Hukumar tsaron Amurka na shan suka

Wasu rahotanni sun nuna cewa hukumar tsaron Amurka ta yi kutse a cikin wasu na'urorin bankunan kasashen duniya, inda ta ga manhajojin da za su kai $2m idan aka sayar da su a kasuwannin shunku.

Rahorannin sun ce hukumar tsaron ta Amurka ta yi kirkiro wasu na'urori da ta yi amfani da wasu , tare da wasu takardu wajen yin kutse a tsarin bankin duniya na intanet.

Masu bincike sun ce irin wannan kutse zai bai wa kasar damar sanya idanu kan harkokin bankunan kasashe.

Wasu bayanai da shafin Shadow Brokers, wanda ke yin kutse a shafukan intanet ya fitar, sun nuna yadda Amurka take kutsen.

Idan har hakan ya tabbata, zai zama babban bayanin da aka kwarmata kan hukumar tsaron Amurka na farko tun bayan wanda mai shafin Wikileaks Edward Snowden ya yi a 2013.

A wani sako da ya wallafa a Twitter, Mr Snowden ya bayyana wannan kwarmato a matsayin "wanda ya fi kowanne girma."

Masu sharhi kan tsaro da dama sun gaskata ikirarin da Mr Snowden ya yi a kan Amurka.