Mayakan IS 90 ne suka mutu a Afghanistan

Aghanistan
Bayanan hoto,

Wannan ne karon farko da aka taba harba irin wannan bom

Jami'ai a Afghanistan sun ce kawo yanzu, akalla mayakan kungiyar IS casa'in ne aka tabbatar sun mutu a hari da shirgegen bom da Amurka ta kai ranar Alhamis.

Sai dai kungiyar ta IS ta musanta cewa an yi mata illa sosai a harin da aka kai a kan hanyoyin karkashin kasa da take amfani da su a lardin Nangarhar.

Har yanzu kuma ba a tattabatar ba ko harin ya shafi wasu kauyukan mutane dake kusa.

Jami'an sojin Amurka da na Afghanistan na ci gaba da hana 'yan jarida da sauran fararen hula zuwa wurin da aka jefa bom din.

Kwamandan sojojin Amurka a Afghanistan, Janar John Nicholson ya ce an harba shirgegen bom din ne bisa yin nazari sosai.