An kashe dalibi saboda batanci ga addini a Pakistan

Pakistan

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Dakunan kwana a jami'ar Abdul Wali Khan dake garin Mardan

Firayiministan Pakistan, Nawaz Sharif ya yi Allah wadai da kisan gillar da wani taron jama'a ya yi wa wani dalibi, bayan an zarge shi da yin batanci ga addini.

Ya ce gwamnati ba za ta amince mutane su rika daukar doka a hannunsu ba, sannan ya bukaci 'yan Pakistan da su hada kansu, su assasa yarda da juna.

Mutanen sun tube wa dalibin mai koyon aikin jarida, Mashal Khan kaya, sannan suka buge shi, tare da harbin shi da bindiga, sannan suka jefo shi kasa ta tagar dakin shi a jami'ar Abdul Wali Khan dake garin Mardan.

Wasu dalibai a makarantar sun yi korafin cewa dalibin, yana da ra'ayi na wadanda ba sa so a rika la'akari da addini a al'amura.

An kama mutane goma sha biyu, kuma jami'an kotu sun ce an tuhumi takwas daga cikinsu da aikata laifin kisan kai da kuma ta'addanci.