Mummunan harin bom ya kashe mutane 40 a Syria

Syria

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mutane na jiran a kwashe su ne lokacin da bom din ya tashi

An kai wani mummunan harin bom da mota cikin kwambar motocin safa a wajen birnin Aleppo na Syria, inda dubban mutane a kauyuka biyu dake hannun gwamnati wadanda aka yi wa kawanya ke jiran a kwashe su zuwa wurin tsira.

Gidan talabijin na gwamnatin Syria ya ce mutane arba'in ne suka mutu.

Wasu hotuna sun nuna gawarwakin mutane da suka hada da na yara a kusa da konannun motoci.

A jiya Juma'a ne aka fara kwashe mutane daga yankin, a karkashin wata yarjejeniya da za a kyale 'yan tawaye 'yan Sunni su fice daga wasu garuruwa biyu a kusa da Damascus, wadanda dakarun gwamnati suka yi wa kawanya.

Wani jagoran 'yan tawaye daga Zabadani ya ce har yanzu yarjejeniyar na nan.

Rahotanni sun ce sojojin Rasha na ba 'yan tawayen da ake kwashewa kariya don kada a kai musu hari na ramuko.