An ba 'yan Afirka 28 izinin zama 'yan Faransa

France

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Shugaban Faransa, Francois Hollande

Shugaban Faransa, Francois Hollande ya ba wasu 'yan Afirka ashirin da takwas izinin zama 'yan kasar, wadanda suka taya Faransa yaki a yakin duniya na biyu da wasu yake-yake.

Shugaban ya ce mutanen, sun zama wani bangare na tarihin Faransa, wacce ya ce suka sadaukar da kansu domin ta.

'Yan mazan jiyan, wadanda shekarunsu ke tsakanin 78 zuwa 90, sun halarci bukin basu izinin zama 'yan-kasa a fadar shugaban kasar.

Duk da cewa akasarin sojoji 'yan Afirkan an mayar da su kasashen su, akwai kimanin dubu daya da har yanzu suke zama a Faransa.

Wata mataimakiyar magajin gari a Paris wacce jika ce ga wani soja dan Senegal wanda ya taya Faransa yakin, ta jima tana kamfe na ganin an ba mutanen karin hakkoki.