'Yadda mahaifina da matarsa ke azabtar da ni'

An fi samun irin wannan halayya a Afirka
Bayanan hoto,

Ana samun matsalolin kuntata wa yaran da iyayensu mata ba sa gida

Wata matashiya 'yar shekara 20 ta ce mahaifinta bisa hadin gwiwar matar uba, yana azabtar da ita, a inda har yake yi mata barazanar korar ta daga gidansa.

Budurwar wadda ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa Amina Aminu ta sashen BBC Media Action Najeriya cewa mahaifin nata ne ya hana ta ci gaba da karatun jami'a, a shekara ta biyu ta karatun nata.

Ta kuma kara da cewa saboda ita marainiya ce ya sa matar uba ke zuga mahaifin nata domin ya rinka ci mata mutunci.

Matashiyar ta ce abin da ya fi bata mata rai shi ne wa'adin kwana biyu da ta fito da miji ko kuma ya kore ta daga gidansa.

Ku saurari yadda hirar matashiyar ta kaya da Amina Aminu:

Bayanan sauti

Matashiyar da mahaifinta ya ke azabtar da ita