Nigeria: Sankarau na yaduwa a yankunan Sokoto

Yanzu haka ana rigafin kamuwa da cutar a cibiyoyin lafiya da ke kasar

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Mutane da dama sun rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar sankarau a Najeriya

A yayin da cutar sankarau wadda ta hallaka daruruwan rayuka a Najeriya ta fara lafawa a yankunan da tafi kamari, bayanai na nuna cewa ana samun karuwar bullar cutar a wasu yankunan da babu ita da farko.

A jihar Sokoto, daya daga cikin jihohin da annobar ta shafa, mazauna wasu yankunan karkara na ci gaba da bayar da rahoton yadda cutar ta fara addabarsu.

Daya daga cikin garuruwan da cutar ta addabe su a yanzu shi ne Achida, wanda ke karamar hukumar Wurno inda ake ake fama da matsanancin zafi.

Mazauna yankin sun ce wannan cuta ta sankarau wadda ba bu ita a garin a da, na kara zama barazana a a garesu, saboda kusan gidaje dai-dai ne ba bu mai cutar a ciki.

Mazauna yankin sun kara da cewa, a mako guda da ya gabata, a kowacce rana sai mutum biyu zuwa uku sun mutu sakamakon kamuwa da cutar ta sankarau.

Bayan garin na Achida, akwai wasu yankunan yankin karamar hukumar ta su ma da cutar ta bulla har ma da rasa rayuka.

A karamar hukumar Gwadabawa , inda da cutar ba ta bulla ba, yanzu haka al'ummar yankin sun ce cutar na addabarsu kwarai da gaske har ma an samu mace-mace a makon da ya gabata.

Alkaluman karshe da hukumomin jihar ta Sokoto suka bayar a kan adadin wadanda suka kamu da cutar a baya dai, ya kai mutum 600, inda 40 daga cikinsu suka rasu.

Jihar ta Sokoto, na daga cikin jihohin Najeriya ta aka samu bullar cutar sankarau a bana, in da jihar Zamfara ta kasance Jihar da annobar ta fi kamari tunda cutar ta barke, inda sama da mutum 200 suka mutu, kuma ake ba wa wasu da dama kulawa a asibitoci da cibiyoyin lafiya.

Tuni dai ma'aikatan kiwon lafiya a Najeriya suka fara rigakafin cutar ta sankarau a wani yunkurin na dakatar da ci gaba da yaduwar cutar.

Kuma nau'in cutar sankarau da aka sani da "meningitis type C" wadda ba a saba samun aukuwar irinta a Najeriya ba ne ya jawo barkewar annobar.