Ana kada kuri'ar raba gardama a Turkiyya

Magoya bayan firaministan Turkiyya Recep Tayyib Erdogan sun ce samun nasararsu a zaben za sa a samu zaman lafiya sosai

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Magoya bayan firaministan Turkiyya Recep Tayyib Erdogan sun ce samun nasararsu a zaben za sa a samu zaman lafiya sosai

Turkawa na kada kuri'a a gabashin kasar a zaben raba gardama wanda zai amince ko akasin haka akan mukamin firaminista da kuma fadada karfin ikon da ya ke da shi.

Yanzu haka sakamakon kuri'un da aka kada ya zuwa yanzu na nuna gagarumin rinjaye a kan mutanen da ke son kawo canji a tsarin dimokradiyyar kasar.

Magoya bayan firaministan kasar, Recep Tayyib Erdogan sun ce shawarar da ya kawo na kara masa karfin iko za ta karawa kasar zaman lafiya da kima a idon duniya.

An dai gudanar da zaben shugaban kasa da wasu manyan zabuka biyu a kasar, a kasa da shekaru uku da suka gabata.