Makami mai linzami ya yi wa North Korea tutsu

Wani sojan Koriya cikin shirin fareti
Bayanan hoto,

Sojojin Koriya ta Arewa sun yi fareti da baje kolin makamai

Wani makami mai linzami da Koriya ta harba ya yi tutsu, bayan da ya tarwatse 'yan dakikai da harba shi.

Sojin Amurka sun ce an harba makamin mai linzami ne daga gabar gabashin ruwan Koriya ta Arewar.

Wannan dai ya biyo bayan wani faretin nuna karfin da Koriyar ke da shi ta fannin soji da kuma baje kolin kayan yaki, a babban birnin kasar Pyongyang, ranar Asabar.

Tuni sojin na Amurka suka ce sun sanar da shugaba Donald Trump kan labarin tutsun makamin.

Da ma mataimakin shugaban, Mike Pence ya je Koriya ta Kudu domin tattaunawa kan yadda za a shawo kan shirin Koriya ta Arewar na samar da makamin nukiliya.

Wutar rashin jituwa tsakanin Amurka da Korea ta Arewa na cigaba da ruruwa.

To amma China na kokarin shiga tsanin domin yayyafawa wutar ruwa.