'Yan ci rani 20 sun nutse a tekun kusa da Libya

migrants

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Dubban 'yan ci rani ne ke yunkurin ketara tekun Bahar Rum a kowacce shekara don shiga Turai

Akalla 'yan ci rani ashirin ne aka tabbatar sun nutse a tekun kusa da Libya, yayin da suke kokarin kai wa ga Turai.

Wani jirgin ruwan Malta wanda ke aikin ceto wani karamin jirgin ruwa dauke da mutane dake bukatar ceto ne ya gano gawarwakin 'yan ci ranin.

A daren ranar Asabar, dakarun Italiya masu gadin gabar teku suka ce an tare mutane fiye da dubu biyar dake tafiya a jiragen ruwa marasa inganci a tekun kusa da Libya.

Ana ganin cewa yanayin zafi da rashin motsawar igiyar ruwa ne suka sa ake samun karin 'yan ci rani dake yunkurin ketara tekun Bahar Rum ta kananan jiragen ruwa.