Mutanen da suka mutu a harin Syria sun haura 120

Syria

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Motocin na dauke da mutane ne da ake kwashe wa zuwa wurin tsira

Rahotanni daga Syria sun ce adadin mutanen da suka mutu a mummunan harin bom kan kwambar motocin dake kwashe mutane daga yankunan da aka yi wa kawanya ya haura dari da ashirin.

Kungiyar kare hakkin jama'ar Syria wacce keda shedkwata a Burtaniya, ta ce daga cikin wadanda suka mutun, akwai akalla yara sittin da takwas.

An kai mummunan harin ne ranar Asabar kan motocin safa da suka fito daga garuruwan Fuaa da Kafraya dake hannun gwamnati, wadanda mayakan 'yan tawaye suka yi wa kawanya.

Har yanzu dai ba san ko wanene keda alhakin kai harin ba.