Mutanen gari sun yi garkuwa da 'yan sanda 32 a Vietnam

Vietnam

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An kama mutane hudu a kauyen ranar Asabar bayan arangama da hukumoi

A Vietnam, mazauna wani kauye na ci gaba da garkuwa da jami'an 'yan sanda talatin da biyu, yayin da ake ci gaba da wata takaddama kan hakkin mallakar wani fili.

Mazauna gundumar My Duc kusa da babban birnin kasar Hanoi, sun kama 'yan sandan ne da yammacin Asabar bayan mutanen garin sun yi arangama da mahukunta a kauyen.

Mazauna kauyen sun ce wani kamfanin sadarwa na rundunar sojin kasar ne ya kwace musu filin ba bisa ka'ida ba, sannan ya sayar ma wani da shi.

Mutanen sun yi garkuwa da 'yan sandan ne bayan an kama wasu mazauna kauyen hudu ranar Asabar.

Daya daga cikin masu fafutuka a kauyen ya ce ba za su sako 'yan sandan ba har sai gwamnati ta sa baki a al'amarin.