'Dole Muhammadou Issufou ya yi murabus'

Tun bayan zanga-zangar da aka yi a makon da ya gabata a kasar, 'yan adawa ke sukar shugaba Muhammadou Issufou
Bayanan hoto,

Tun bayan zanga-zangar da aka yi a makon da ya gabata a kasar, 'yan adawa ke sukar shugaba Muhammadou Issufou

A jamhuriyar Nijar, har yanzu mummunar zanga-zangar da ta yi sanadiyar mutuwar wani dalibi a Yamai a ranar Litinin din da ta gabata na ci gaba da jawo ce ce ku ce a kasar.

Bayan kungiyoyin farar hula, kawancen da ke mulki ne ya fitar da sanarwa domin nuna damuwarsa game da abin da ya faru.

Kawancen jam'iyyun da ke mulki a kasar da ya kunshi sama da jam'iyyun siyasa hamsin, ya nuna rashin jin dadinsa game da abinda ya faru sakamakon zanga-zangar da dalibai a jami'ar Yamai suka yi a ranar goma ga watan da muke ciki.

Wannan zanga-zanga dai ta yadu a wasu sassa na kasar musamman a jami'ar Maradi in da har dalibi guda ya rasa ransa.

Bayan rasa rai da aka yi sakamakon zanga-zangar, an kuma lalata kadarorin gwamnati da ma na wasu bayin Allah.

Kazalika kuma an raunata wasu masu zanga-zangar da dama, yayin da kuma aka kama wasu daga cikinsu.

'Ya'yan jam'iyyar PNDS mai mulki a kasar ma sun bayyana rashin jin dadinsu game da abinda ya faru, amma kuma sun ce bai kamata 'yan kasa su rinka karya doka ba, wajibi ne su bi doka.

Tun bayan zanga-zangar dai, kungiyoyin farar hula da na ma'aikata da ma kungiyoyin 'yan siyasa da suka hada da na 'yan adawa suke ta Allah wadai, da kuma kira ga gwamnatin da ta dauki matakan kyautata ilimi a kasar.

Wani kawancen farar hularma kira ya yi ga shugaban kasar Muhammaduo Issufou, a kan ya yi murabus, tun da ya gaza a aikinsa.