Lokacin daga wa Koriya ta Arewa kafa ya wuce — US

Mike Pence ya ce lokacin daga wa Koriya ta Arewa kafa ya wuce

Asalin hoton, AFP/GETTY IMAGES

Bayanan hoto,

Mike Pence ya ce lokacin daga wa Koriya ta Arewa kafa ya wuce

Mataimakin shugaban kasar Amurka, Mike Pence, ya yi gargadin cewa an kammala daukar dukkan matakan da za ayi maganin Koriya ta Arewa.

Yana wannan bayanin ne a yayin da ya kai ziyara wata iyaka da ke da tarin sojoji da ke tsakanin Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu.

Mr Pence, ya ce yanzu lokacin daga wa Koriya ta Arewa kafa ya wuce.

Kuma dama shugaba Trump ya bayyana karara cewa ba zai tattauna da kowa ba a kan matakin da za a dauka kan Koriya ta Arewan ba.

Mr Pence, ya cigaba da cewa akwai dangantaka mai karfi a tsakaninsu da Koriya ta Kudu.

Tun da farko, mataimakin shugaban Amurkan, Mike Pence ya isa Seoul babban birnin Korea ta Kudu, bayan wasu 'yan sa'o'i da Koria ta Arewa ta yi rashin sa'a a gwajin makaminta mai linzami da ta yi.