'Bikin Easter ya fi na Kirsimeti zama wajibi'

Easter

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan katolika da Angilikan suna yin azumi kafin ranar Easter

Fasto Yohana Buru wanda limamin addinin kirista ne a jihar Kadunan Najeriya, ya ce bikin Easter ya fi na kirsimeti lada ga kiristoci na hakika.

Ya ce kirsimeti ba lallai ba ne kuma wasu kiristocin ma ba suna danganta bikin da bidi'a, a inda ya ce ranar Easter ita ce ma fi daukaka.

Fasto Buru ya kara da cewa a ranar Easter ne aka gicciye Yesu Almasihu saboda haka ya kamata duk wani kiristan da ya amsa sunansa ya tuna da wannan ranar kasancewar Yesu ya mutu ne domin fansar zunuban al'ummarsa.

Wasu kiristoci mabiya mazahabar Katolika da Angilikan sukan kwashe kwana 40 suna yin azumi domin tarbar wannan rana.

Sai fasto Yohana ya ce ba lallai ne ba kowane kirista sai ya yi haka.

Ku saurari fasto Yohana Buru a hirarsa da Nura Ringim:

Bayanan sauti

Fasto Yohana Buru