Sojojin Nigeria sun ceto mutum 1,623 daga Boko Haram

An kai mutanen sansanin 'yan gudun hijra
Bayanan hoto,

Sojoji sun ceto mata da kananan yara

Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta bisa hadin gwiwar 'yan sintiri sun ceto mutane 1,623 daga hannun 'yan Boko Haram, bayan sun fatattaki 'yan kungiyar a jihar Borno.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin, Birgediya Janar Sani Usman Kuka-Sheka ya fitar, ta ce sojojin sun yi aiki ne da wani bayanin sirri na maboyar 'yan kungiyar a yankin Jarawa ta karamar hukumar Kala Balge.

Sanarwar ta ce sojojin suna shiga kauyen na Jarawa sai aka bude musu wuta, a inda sojojin suka mayar da martani.

Daga nan ne kuma sojojin suka shiga kauyukan Deima da Artano da Saduguma da Duve da Bardo da Kala da Bok da Msherde da kuma Ahirde, domin fatattakar 'yan kungiyar.

Sanarwar ta ce sojojin sun samu nasarar kashe 'yan Boko Haram 21, baya ga ceto mutanen 1,623 da suka hada da mata da kananan yara.

Yanzu haka dai kamar yadda sanarwar ta ce, tuni aka kwashi mutanen 1,623 zuwa sansanin 'yan gudun hijra da ke Rann, bayan an diga wa kananan yara allurar rigakafi.

Bayanan hoto,

An kai mutanen sansanin 'yan gudun hijra na Rann