Nigeria: Ana karkatar da akalar maganin cutar sankarau

Maganin cutar sankarau da allurar rigakafinta duk kyauta ne a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Maganin cutar sankarau da allurar rigakafinta duk kyauta ne a Najeriya

Alkaluman hukuma a jihar Zamfaran Najeriya, sun nuna yawan wadanda cutar sankarau ta hallaka a jihar kawai, ya karu zuwa mutum 350 da ga 215 a cikin makonni biyun da suka gabata.

Haka ma yawan wadanda suka kamu da cutar ya karu zuwa mutum 3,200 daga 1,800 a cikin wannan lokacin.

Wadannan sabbin alkaluman sun fito ne a dai-dai lokacin da hukumomin jihar suka kaddamar da bincike kan zargin karkata akalar magungunan cutar a wasu asibitoci.

Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Abdullahi Muhammad Shinkafi, ya shaida wa BBC cewa, sun samu korafi daga kananan hukumomin jihar Uku in da ake sayar da maganin cutar ta sankarau ga marassa lafiya, maimakon kyauta.

Dan haka ne gwamnatin jihar, ta kafa wani kwamiti na musamman domin ya gudanar da bincike a kan gaskiyar lamarin.

Kuma, yanzu gwamnati ta dauki matakai ciki har da jami'an tsaro, da kuma gudanar da bincike a kan zargin karkatar da akalar magungunan.

Farfesa Abdullahi Muhammad Shinkafi, ya ce duk wanda aka gano da karkatar da akalar maganin, to ko shakka ba bu za a hukunta shi gwargwadon abinda doka ta tanada.

Daga karshe, sakataren gwamnatin jihar ya ja hankalin masu irin wannan halayya ta karkatar da maganin cutar ta sanakarau da su ji tsoron Allah su dai na.