Facebook zai hana dora munanan bidiyo

Ba wannan ne karon farko da Steve Stephens ya kashe mutum ba

Asalin hoton, FACEBOOK

Bayanan hoto,

Ba wannan ne karon farko da Steve Stephens ya kashe mutum ba

Shafin sada zumunta na Facebook ya ce ya na nazari a kan hanyar da zai bi wajen magance yadda ake sanya hotunan bidiyo ko wasu abubuwa da suka saba da nagartarsa.

Facebook ya sanar da hakan ne bayan sanya wani hoton bidiyon kisa a shafin na tsawon sa'oi biyu.

Shafin ya ce ba zai bata lokaci ba a kan nazarin hanyoyin da zai bullo da su ba.

A ranar Lahadi ne, wani mutum ya sanya hoton bidiyon kisan da ya yiwa wani tsoho a Cleveland da ke jihar Ohio ta Amurka.

Tun dai bayan da Steve Stephens mai shekara 37 ya fada da bakinsa a wani sabon bidiyon kai tsaye a shafin Facebook, cewa shi ne ya kashe Robert Godwin, mai shekara 74, 'yan sanda suka baza komar farautarsa.

Steve ya kuma ce ya kashe mutane 13 ta irin wannan hanya duk da cewa 'yan sandan sun ce ba su da masaniyar hakan.

'Yan sanda dai sun alkawarta bayar da ladan dala dubu 50 ga duk mutumin da ya bayar da bayanin da ka iya sanya a gano da kama Steve.

Hoton kisan dattijon da Steve ya yi dai ya janyo kakkausar suka daga jama'a.