North Korea: Za mu iya fara kai wa Amurka hari

Kakansa, Kim II-sun ne ya kafa kasar
Bayanan hoto,

Kim Jong-un ya gaji mahaifinsa

Wani babban jami'in gwamnatin kasar Korea ta Arewa, ya ce kasar tasa za ta iya fara kai wa Amurka hari idan ta ga alamun Amurkar na shirin kai mata hari.

Yayin wata tattaunawa da BBC, Mataimakin ministan harkokin waje na Koriya ta Arewar, Han Song Ryol, ya ce za su tsinduma yaki da zarar Amurka ta kuskura ta kai musu hari.

Mista Song Ryol ya ce "idan Amurka tana shirin kai mana harin soji, to ta san da sani za mu mayar da martani da makamin nukiliya ta irin tsarin kai hare-harenmu."

Ya kuma kara da cewa yanzu haka kasar tasa za ta rinka gudanar da gwaje-gwajen makamai masu linzami a kowane mako da wata da kuma a duk shekara.

Mataimakin shugaban Amurka, Mike Pence dai ya gargadi Koriyar da ta kuka da kanta ka da ta tuke Amurkar ta hanyar cigaba da shirin samar da makamin nukiliya.

A ranar Lahadi ne dai mista Pence ya je Koriya ta Kudu bayan wani makami mai linzamin da Koriya ta Arewa ta harba ya yi tutsu.

Ita dai koriya ta Kudu ta zama tamkar juji a wajen makwabciyartata Koriya ta arewa ta fannin gwaje-gwajen makamai.

Rahotanni dai na cewa Amurkar ta daddasa na'urorin a Koriya ta Kudu wadanda za su hana makaman da Koriya ta Arewa za ta harba yin tasiri.

Koriya dai tana shirin samar da makamin nukuliya, abin da ya sabawa dokokin majalisar dinkin duniya.

Ana dai tsammanin kasar da dab da cimma makami mai linzami mai dogon zango da zai iya tankarar da Amurka.

To sai dai shugaban Amurkar, Donald Trump ya ce ba za ta su bari hakan ya faru ba.