Ronaldo ya zarce sa'a a gasar Zakarun Turai

Cristiano Ronaldo
Image caption Ronaldo ya ci wasa goma cikin 12 a zagayen daf da kusa da na ƙarshe da Real Madrid ta buga a gasar cin kofin Zakarun Turai

Ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa na Real Madrid, Cristiano Ronald ya ci ƙwallonsa ta ɗari a gasar cin kofin Zakarun Turai.

Da wannan gagarumin abin tarihi, Ronaldo ya zama ɗan wasa na farko da ya ci ƙwallo ɗari a gasar.

Daga bisani, ya ƙara jefa ƙwallo a ragar Bayern Munich, inda ya haɗa ƙwallo uku a karawar da suka yi cikin daren Talata.

Yanzu dai Real Madrid ta yi nasarar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe.

Ronaldo ya zarce sa'a....

  • Ƙwallo ukun da Cristiano Ronaldo ya ci ta sanya shi zama ɗan ƙwallon ƙafa na farko da ya ci ƙwallo 100 a gasar Zakarun Turai
  • A dai wannan dare ne, maƙwabtan Real wato Atletico su ma suka yi nasarar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar.
  • Madrid ta samu cancantar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar Zakarun Turai karo bakwai a jere - ƙwazo mafi tsayi a tarihin gasar.
  • An cinye Bayern Munich gida da waje karon farko a gasar cin kofin Zakarun Turai tun bayan 2014, lokacin da Madrid ta lallasa su da ci 5-0 a zagayen kusa da ƙarshe
  • Sau tara kenan Ronaldo yana cin Bayern Munich a gasar Zakarun Turai - Lionel Messi na Barcelona ne kaɗai ya ci wata abokiyar fafatawarsu fiye da shi (wato Arsenal)
  • Lewandowski ya jefa ƙwallonsa ta shida a ragar Real Madrid a gasar Zakarun Turai.
  • Jan katin da aka ba wa Arturo Vidal shi ne na sha tara da aka ba wa wani ɗan wasan Bayern Munich a gasar Zakarun Turai - ko da yake, Juventus ta fi ta da yawan jan kati (22)

Labarai masu alaka