Ka san yadda za ka yi maganin warin tafarnuwa?

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Duk da tsananin warin tafarnuwa, cin wasu 'yan ganyayyaki kamar na'ana ko salak ko tuffa kan yi maganin warin

Tafarnuwa kamar yadda masu cin burodi da wasu kayan abincin da ake yi da ita suka sani tana da warin da ke dadewa sosai a jikin mutum tsawon lokaci bayan ma ya manta da ya ci abin. Ko me ya sa hakan? kuma ka san da cewa akwai 'yan ganyayyakin da za ka hada ta da su ka kashe warin?

Za ka ga har bayan sa'a a 24 bayan cin abin da aaka yi ta ita warin tafarnuwar yana nan a gumin mutum da ma numfashinsa. Abin yakan kai ba ma sai mutum ya sanya ta a bakinsa ba, kafin ka ji numfashinsa yana warinta.

A shekarar 1936 likitoci sun wallafa a mujallar kungiyar likitoci ta Amurka, (Journal of the American Medical Association), cewa, bayan 'yan sa'o'i an ji warin tafarnuwa a numfashin wani maras lafiya da aka ba wa miyar tafarnuwa ta hanyar irin robar nan ta durawa maras lafiya magani ko abinci ta hanci.

Haka kuma wani likitan ma ya rubuta cewa, shi ma ya hadu da irin wannan abin, inda ya ji warin tafarnuwa mai karfi lokacin da yake karbar haihuwar wata mata.

Ya ce bayan wani dan lokaci kadan da haihuwar, ''abin mamaki sai na ji warin tafarnuwa a numfashin ita ma jaririyar.'' Ya ce, wani lokaci idan ya gaya wa mutane abin sai su dauk wasa kawai yake.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Tafarnuwa tana shiga cikin jini, saboda haka ne warinta yake dadewa a jikin mutum

To abin da ya sa ake jin warin tafarnuwa daga jikin wadanda ba su taunata ba, kamar maras lafiyar da aka dura masa miyarta zuwa cikinsa ta roba da kuma jaririyar da mahaifiyarta ce take cin tafarnuwar shi ne, tafarnuwa tana da wasu sinadarai ne (sulphur) da ke shiga cikin jinin mutum bayan jiki ya sarrafa ta.

Daga cikin jinin ne, suke shiga cikin huhu har su kai ga makogwaro sannan kuma su zo bakin mutum. Duk yadda ka wanke bakinka ba za ka iya raba shi da warinta ba, domin warin ba daga bakin yake ba, daga aikin da kayan cikinka suke yi yake samuwa.

Tun da haduwar sinadaran da tafarnuwar ke dauke da su ne, da kuma aikinsu daga wannan sashe na cikin mutum zuwa wancan sashe, ke haddasa warin, to hanyar da ta fi dacewa a yi maganin warin, ita ce ta irin wannan hanya ta kimiyya.

Wata masaniyar kimiyya a Jami'ar Jihar Ohio ta Amurka, Sheryl Barringer, wadda ke nazari a kan yadda kwayoyin halitta na sinadarai ke taimakawa wajen samar da dandano, ta ce wata dalibarta ta nemi gudanar da bincike a kan numfashi da warin tafarnuwa.

Akwai binciken da aka yi wanda aka gano wasu kayan abincin da idan aka ci tare tafarnuwa, suke batar da warinta. Kayan abincin da suka fi yin hakan sun hada da ganyen salak (lettuce), da dankali, da na'ana da sauransu. To amma fa ba a san dalilin da ya sa wadannan abubuwa suke kashe warin tafarnuwar ba idan an ci su tare.

Tun daga sannan ne Barringer da wasau daliban suka dukufa wajen gano wannan sirri na yadda wasu kayan abinci ke maganin warin na tafarnuwa.

Salak da na'ana da kuma abin mamaki tuffa, wadda Barringer ta ce bisa kuskure suka gano cewa ita ma tana kashe warin tafarnuwa.

An gano hakan ne, lokacin da wani dalibi da ya sha ruwa bayan ya ci tafarnuwa, sai kawai ya ji warinta ya ragu. Daga nan ne sai ya fara bibiyar abubuwan da ya ci a baya tun lokacin da ya ci tafarnuwa a ranar, inda ya tuna cewa ai ya ci tuffa.

Haka kuwa aka yi sai aka jarraba hakan, inda aka ci tuffa bayan an ci tafarnuwa, sai kuma abin mamaki aka ji warin tuffar ya ragu.

A kasidar baya-bayan nan da daliban suka fitar a watan Satumba na shekarar da ta wuce, sun bi diddigin yadda wadannan abubuwa suke kashe warin tafarnuwar, inda suke ganin gwamutsuwar da wasu kwayoyin sinadaran halitta da ke cikin tafarnuwar ne na sinadarin farar-wuta (sulphur) da wasu kwayoyin halittar sinadarai.

A gwajin da daliban suka yi sun gano cewa ganyayyakin da ke kashe warin tafarnuwar sun fi tasiri idan aka ci su danyu, ba tare da an dafa su ba.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Tuffa na daya daga cikin abubuwan da ke rage tsananin warin tafarnuwa

Barringer ta ce daga ganyayyakin da suka yi gwajin da su, na'ana ta fi tasiri, domin ta fi yawan sinadaran kwayoyin da suke kashe warin na tafarnuwa (phenolics). Tuffa ba ta da wadannan sinadarai da yawa amma kuma duk da haka tana dan ragewa. Shi kuwa ganyen salak kamar yadda suka gano shi ne mafi karancin wadannan sinadarai, inda hatta koren gnyen shayi ma ya fi shi, wanda ma ba shi da wani kanshi sam-sam.

Wannan ne ya sa Barringer ta ce, '' abin da ya sa kenan na ce ba mu fahimci abin da yake haddasa wannan abu ba gaba daya ma.''

To amma duk da cewa ba a kai ga fahimtar yadda abin ke aukuwa ba, duk da haka za ka iya amfani da wasu daga cikin wadannan ganyayyaki da sauransu wajen kawr d warin tafarnuwa.

Amma kuma mu kwana da sanin cewa fa, ba ta yadda duk wani hade-haden kanshi da za mu yi, zai iya sauya mutum daga matsayinsa na cewa shi dan adam, wata ma'aikata ce mai rai da kuma fitar da numfashi.

Abubuwan da muke fitarwa ta numfashi ko ta guminmu (zufarmu), za su iya nuna ba ma abin da muka ci ba tun jiya kawai, hatta wasu kwayoyin bakteriya da suka yi kama-wuri-zauna a bakinmu, tare da bayyana ko ma muna dauke da wasu cutuka.

Masana kimiyya a yanzu suna nazari kan yadda za su iya gano cewa ko mutum yana dauke da alamun wata cutar daji a jikinsa, ta hanyar kwayoyin kanshi ko wari da ke cikin numfashinsa

Yayin da dan adam yake fafutukar magani ko boye duk wani wari da ke fitowa daga jikinsa, yana da muhimmanci ya san cewa fa, abin nan da yake kokarin boyewa ka iya kasancewa wani abu ne mai muhimmanci da bai san sirrin da ke cikinsa ba.