Ka san tsutsar da ake sayar da tarin kilo daya naira miliyan takwas ?

Tsutsa mai daraja a China Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A China an yi amanna tsutsar na maganin cutuka da yawa, kamar asma da sankara

Nawa za ka iya biya domin cin wata tsutsa da ake abinci da ita? Na tabbata dai in har ka yadda ka ma iya kallonta, ba lalle ne ka yarda ka biya kudin da ya kai abin da yawancin masu hali a China suke biya ba, wanda ya kai kusan naira miliyan takwas a kan kilo daya na wannan tsutsa da ake maganin cutuka ba.

Veronique Greenwood ta yi mana bincike a kan wannan abin mamaki

Idan ka tunkari wani shago da ke kusa da kofar wani babban kantin sayar da kayan abinci a kudancin China, abin da za ka gani na yi maka maraba shi ne tarin wata busasshiyar tsutsa na jiran mai cefane.

Wannan zai iya kasancewa wani sashe ko bangare na kasar ta China, inda mutane ke bugun kirjin cewa za su iya cin komai da ke da kafa biyu, in dai ba mutum ba ne, da kuma duk wani abu mai kafa hudu, in ba tebur ba ne - kamar dai yadda mutanen Texas ke da nacin son balangu, sai dai a wannan karon, tsutsa ce mutanen ke matukar sha'awar ci.

Wannan tsutsa wadda ana samunta ne a Tibet da yankin Himalaya, ta samu wannan daraja ne saboda a fannin maganin gargajiyar China an yi amanna tana maganin kusan duk wata cuta kama daga asma zuwa daji.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yadda wani mutum ke neman tsutsar kenan a surkukin tsaunukan China

Haka kuma ana ganin tana da wannan daraja ne domin tana sa wanda yake da ita fita daga sahun marassa hali, domin ana sayar da kilo daya nata a kan sama da dala dubu 20, kwatankwacin naira miliyan takwas, ko ma sama da haka.

Ita dai wannan tsutsa mutane sun fara nemanta ne can a yankin Tibet, wato a nisan dubban mila-milai daga Chinan, inda mutane kan shafe tsawon lokacin kowace damuna, gurfane a kasa suna faman neamn tsutsar a kan tsaunuka.

Za a iya samun cikakken labarin yadda ake farautar wannan tsutsa inda Michael Finkel, ( National Geographic), ya yi rubutu kan zuwa Tibet domin ganin yadda ake samunta shi da kansa, a 'yan shekarun da suka gabata.

Wani miji da mata da Finkel ya bi domin ganin yadda abin yake, sun sayar da guda 30 da suka samu da kyar a kan dala 90, amma kuma a birane, rabin kilo daya na wadda take da kyau sosai zai iya kaiwa dala dubu 50, kamar yadda Finkel ya rubuta.

Ba wai ana cin tsutsar ba ne da yawa a lokaci daya. Mutane suna tsuma su ne a ruwa dai-dai ko bibbiyu, sai su rika sanya su a cikin miya ta magani.

Ana sayar da tsutsar ne a kantinan kayan abinci, a Chinan tare da sauran nau'in kwari na ruwa wadanda suke da daraja suma, wanda hakan ya sa irin wadannan kwari kamar sauran dabbobin dawa da ake amfani da wasu sassan jikinsu, suke fuskantar barazanar karewa a duniya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana sayar da kilo daya na busasshiyar tsutsar har dala dubu 20, kusan naira miliyan takwas

Farautar tsutsar ba sauki ba ce ga su kansu mutanen domin wasu mutane biyu sun kai ga rasa ransu sakamakon rikici a kan tsutsar a Nepal a shekara ta 2010.

Sai dai a wani rahoto na CNN a 2016, an nuna cewa kasuwar tsutsar za ta iya faduwa sakamakon shirin yaki da cin hanci da rashawa da ake shirin bullowa da shi yanzu a China, domin duk wani jami'in gwamnati da aka samu da tarin tsutsar, kamar yadda ake ba su tukuici, ka iya jefa shi cikin matsala maimakon samun kudi.

Haka kuma bisa ga dukkan alamu, yanzu tsutsar na kara yin karanci da wahalar samu kamar yadda, dan jarida mai daukar hoto na kamfanin Getty, Kevin Fryer, wanda ya mayar da hankali kan labarin, ya yi tattaki domin ganin yadda neman yake a yanzu, inda ya gano cewa a wuraren da a da mutane suke samun guda 500 a rana, yanzu bai wuce su samu hudu ko biyar ba.

Yanzu dai za a zuba ido ne a ga yadda za ta kasance ga tsadar farashin tsutsar, da ita tsutsar kanta da kuma su kansu al'ummomin da suke dogaro da kudin da suke samu daga cinikinta.

Kafin sannan a yanzu dai wannan harka ta samar da wannan nau'in tsutsa na ci gaba da samar da makudan kudade ga wadanda ke yinta a shagunan sayar da kayan abinci a China.