Babban kada ya hadiye mafarauci a Zimbabwe

Babban Kada a Zimbabwe Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Nile crocodiles lurk almost totally submerged in the water as they lie in wait for passing prey

A kasar Zimbabwe, wani gwajin kwayoyin halittu da aka yi ya nuna cewa sassan jikin mafaraucin da ya yi batan dabo shi ne a cikin wani babban kada da aka hallaka.

Mafarauci dan kasar Afirka ta Kudu Scott Van Zyl da ya yi batan dabo ne a makon jiya lokacin da ya ke farautar kadan.

Wani mai gudanar bincike ya shaidawa BBC cewa Mr Van Zyl kwararren mafarauci ne da ya gamu da bacin rana a lokacin da ya yi bulaguro zuwa kan iyakar Afirka ta Kudu da Zimbabwe don yin farauta.

A makon jiya ne Scott Van Zyl ya gamu da ajalinsa a gabar kogin Limpopo , kamar yadda Sakkie Louwrens, daraktan wata kungiya mai zaman kanta dake yaki da aikata maynayn laifuka ta Afirka ta Kudu.

Mutuwarsa ita ce ta baya bayan nan a irin munanan hare-haren da manyan kadoji ke yi a Zimbabwe.

Hakkin mallakar hoto Heritage Protection Group
Image caption Kwararren mafaraucin Scott Van Zyl ya yi batan dabo ne a makon jiya a Zimbabwe

Mr Louwrens ya shaidawa BBC cewa Mr Van Zyl ya yi bulaguron yin farauta ne a kan iyakarakasashen Zimbabwe da Afirka ta Kudu da wani dan yankin mai yi masa jagora da kuma wasu tarin karnuka.

Ya ce mutanen sun ajiye motarsu kana suka nufi wani wuri na daban don neman kadoji.

Bayan da karnunan Mr Van Zyl suka dawo sansaninsu ba tare da shi ba ne, masu aikin bincike da ceto suka bazama.

An kuma ga alamun sawayen mafaraucin ne a gabar kogin da jakar goyonsa a yashe.

Mr Van Zyl na da mata da 'yaya biyu.

Mr Louwrens ya ce wani ma'aikacin kungiyar karewa da lura da kayyakin tarihi-- kungiyar da yake jagiranta da kuma aiki da 'yan sanda yaki da aikata muggan laifuka a Afirka ta Kudu--ya taimakwa mahukuntan kasar ta Zimbabwe ajen gudanar da binciken.

Ya ce don kokarin gano mafarucin, an bayar da izinin harbe nauiun manyan kadoji uku a yankin, kuma daya daga cikinsu na dauke da sauran sassan jikin Mr Van Zyl a cikinsa.

Ya ce kuma ce gwajin kwayoyin halittu sun sake tabbatar da hakan.

Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Babban Kada na Afirka daya daga cikin mafi hadari ne a duniya

Munanan hare-haren manyan kadoji hudu ne aka bada rahoton faruwarsu a kasar Zimbabwe cikin wannan shekarar.

Wata kungiyar raya gandun daji a yankin ta yi Allah wadai da irin abinda ya haddasa mutuwar mutumin

" Tun farko ma bai kamata ba ma ya je wannan farauta.'' In ji kungiyar.

Ta kuma ce duk dabbar da ke daji..kawai ka bar ta a matsayinta a daji, a koda yausge suna tunanin yadda za su rayu ne.

Labarai masu alaka