Sai zankaɗeɗiyar mace za a ɗauka hadimar jirgin sama?

Aeroflot attendees Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hadiman jirgin saman Aeroflot, kamfanin yana kallonsu a matsayin fuskar harkokinsa

Babban kamfanin sufurin jirgin saman Rasha na fama da wata ƙara da ma'aikatansa mata suka shigar, inda suka ce ya fi fifita zuƙeƙiyar mace siririya wajen ba da aikin hadiman jirgi.

A ranar Talata ne wata kotu a birnin Moscow ta yi watsi da iƙirarin da wata ma'aikaciyar jirgi, Irina Ierusalimskaya ta yi cewa kamfanin yana nuna wariyar jinsi.

Tana shirin ɗaukaka ƙara, inda take samun goyon bayan wani fitaccen mai fafutukar kare haƙƙin ɗan'adam a Rasha kuma jami'in ƙwadago, Boris Kravchenko.

Kamfanin ya ce duk wani ƙarin nauyin kilogram na tilasta masa ƙarin kashe kuɗi kan man jirgi.

A takardar kamfanin na ɗaukar ma'aikata, Aeroflot na buƙatar mace su bayar da bayanin tsayi da nauyi da kuma girman tufafin da take sanyawa.

Sai ma'aikaciya ta cim ma tsayin da ake buƙata saboda su ne ke sanya wa fasinjoji jakunkunansu a wajen ajiyar kaya a cikin jirgi, in ji Aeroflot.

'Fuskar kasuwancin Rasha'

Nan gaba kuma kotun za ta saurari makamanciyar wannan ƙara daga wata ma'aikaciyar Aeroflot, Yevgenia Magurina.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kamfanin yana zuba maƙudan kuɗi wajen sayen ƙarin jirage da bunƙasa tallace-tallace

Wani jami'in Aeroflot ya faɗa wa kotu cewa "Idan jikin mace ya kara nauyi, zai zama abu mai wahala ga ma'aikaciya ta iya kurɗawa a cikin jirgi don hidimta wa fasinja."

Sanarwar kamfanin ta ce "Mata hadiman jirgi su ne fuskar kowanne kamfani, kuma tamkar wani kati ne da ke ba da bayanan harkokin kasuwancin ƙasa".

A wannan mako ne, wani babban kamfanin harkokin tuntuɓa na ƙasashen duniya, Brand Finance ya bayyana kamfanin jirgin saman Aeroflot a matsayin "hamshaƙin kamfanin" Rasha.

Rahoton Brand Finance a kan Rasha ya ce Aeroflot "ayarin jirage mafi sabunta idan an kwatanta da duk manyan kamfanonin jirgin sama kuma yana zuba dukiya wajen harkokin talla, musammam ma a nahiyar Asiya".

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gwamnatin Rasha dai tana da taƙaitaccen jari a kamfanin wanda aka kafa tun zamanin Sobiyat

Gargaɗin ƙungiyar ƙwadago

Aeroflot ya inganta harkar tarairayar abokan hulɗarsa tun bayan zamanin tarayyar Sobiyat, lokacin da aka fi tsokanarsa kan hadiman jirgi masu ɗaure fuska da abinci maras ɗanɗano.

Sai dai Boris Kravchenko ya bayyana shari'ar Ierusalimskaya da cewa "ƙara ce da ba a taɓa ganin irinta kan wariyar jinsi".

Kravchenko dai wakili ne a majalisar kare haƙƙin ɗan'adam ta shugaba Vladimir Putin kuma jagora ne na haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago ta Rasha.

Yayin zantawa da kafar yaɗa labaran Rasha ta RBC News, jami'in ya yi gargaɗi kan yiwuwar tsunduma yajin aiki "matuƙar irin wannan nuna bambanci ya ci gaba"

A kotu, jami'in Aeroflot ya ce duk wani ƙarin nauyin kilogram na sanya kamfanin kashe ƙarin kuɗi rubul 800 kwatankwacin naira 5,500 duk shekara wajen sayen man jirgi.

Ya kuma ce a wani nazari da aka gudanar, kamfanin Aeroflot ya gano cewa fasinjoji sun fi son hadiman jirgin 'yan ƙwalisa.

'Ba aikin jibgegiyar mace ba ne'

Misis Ierusalimskaya 'yar shekara 45 na son kamfanin ya biya ta diyyar rubul miliyan 1 kwatankwacin dala 17,750, a cewar kafar yaɗa labaran Rasha Kommersant.

Hadimar jirgin wadda ke sa riga mai lamba 52 (wato ƙatotuwa a ƙarƙashin tsarin tufafi na duniya).

Ta ce kamfanin ya yi mata sauyin wajen aiki inda ya mayar da ita ɓangaren jiragensa masu jigila a cikin gida, kuma ya zaftare mata kuɗin shiga.

Ta yi ƙorafin cewa dokokin Aeroflot na buƙatar hadiman jirgi su kasance masu tsayin aƙalla santimita 160 (5ft 3ins) kuma girman rigarsu kada ya wuce 48.

Labarai masu alaka