Majalisar dattijan Nigeria ka iya mayar da Ndume

Bukola Saraki Hakkin mallakar hoto OTHER
Image caption Bukola Saraki ya ce shawarar dakatar da Ndume ko janye dakatarwar ba ta mutum ɗaya ba ce

Shugaban majalisar dattijai a Nijeriya, Sanata Bukola Saraki ya ce ana gudanar da tuntuɓa a bayan fage don ganin an janye dakatarwar da aka yi wa Sanata Ali Ndume.

Yayin wata zantawa da ya yi da BBC, Bukola Saraki ya ce "ya yi yaƙini akwai abin da zai faru idan majalisar ta koma aiki."

"Na tabbata za a ci gaba da tattaunawa idan muka koma zaure majalisa... Abu ne da kowa zai so ya ga an daidaita."

A ƙarshen watan Maris ne Majalisar dattijan Nijeriya ta dakatar da Ndume wanda tsohon shugaban masu rinjaye ne sakamakon kiran da ya yi don a binciki zargin da ake yi wa shugaban majalisar da kuma Sanata Dino Melaye.

Sai dai bayan kammala bincike, sai kwamitin ɗa'a na majalisar ya wanke Bukola Saraki daga zargin shiga da mota ƙasar ba bisa ka'ida ba, da kuma Dino Melaye kan amfani da takardar shaidar digiri na bogi.

Sanata Ali Ndume ya daɗe yana takun-saka da shugaban majalisar, Bukola Saraki amma abin ya fito fili lokacin da aka sauke shi daga mukamin shugaban masu rinjaye.

Ya ce zargin cewa saboda abin ya shafe shi ne aka dakatar da Ali Ndume, duk ba haka ba ne, magana ce da kwamitin ɗa'a ya gudanar da bincike a kanta.

Bukola Saraki ya ce a matsayinsa na shugaban majalisa ba shi da ikon ɗaukar wani mataki a kan wani ɗan majalisa don kawai, yana jin an tsane shi.

A cewarsa tsarin dimokraɗiyya zai ƙarfafa ne idan ana bin ƙa'ida ko da kuwa wani tsari bai yi wa mutum daɗi ba.

Ya ce sanata Ndume ya san hanyoyi gabatar da ƙorafe- ƙorafe irin waɗannan, ba tare da an tozarta majalisa ba.

Labarai masu alaka