Akwai rashin jituwa tsakanin Buhari da Saraki?

Saraki ya ce ba zai taba kunyata Buhari ba Hakkin mallakar hoto Nigeria senate
Image caption Saraki ya ce ba zai taba kunyata Buhari ba

Akasarin 'yan Najeriya na ganin bangaren zartarwa da na majalisar dokokin tarayya, karkashin jagorancin Sanata Bukola Saraki na zaman doya da manja ne kawai, musamman ganin irin ce-ce-ku-cen da bangarorin biyu suka rika yi tun farkon shigowar gwamnatin.

Sai dai tambayar da kowa ke son sanin amsarta ita ce: shin akwai sabani tsakanin Shugaban kasar Muhammadu Buhari da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, ko dai kawai 'yan siyasa ne ke son raba kawunan manyan jami'an gwamnatin biyu?

Alamar farko da ta nuna cewa za a samu baraka tsakanin Shugaba Buhari da Sanata Saraki, ita ce bijirewar da Saraki ya yi wa jam'iyyarsu ta APC inda ya tsaya takarar shugabancin majalisar dattawa, duk da cewa jam'iyyar ta fitar da wanda take so 'yan majalisar su zaba -- Sanata Ahmad Lawan.

Hadin kan da wasu Sanatocin jam'iyyar APC suka yi da takwarorinsu na jam'iyyar hamayya ta PDP inda suka zabi Sanata Saraki a matsayin shugaban majalisar, ya sa 'yan kasar da dama na ganin Saraki ba zai rika aiwatar da abubuwan da gwamnatin Buhari ke so ba.

Hakan ne ma ya sa lokacin da kotun da'ar ma'aikata ta soma yi wa Sanata Saraki shari'a kan zargin yin karya wajen bayyana kadarorin da ya mallaka, 'yan kasar da dama ke ganin yana girbe abin da ya shuka ne.

Wasu kuma na yi wa Saraki kallon yana hankoron kujerar Shugaba Buhari a zaben 2019, batun da ya sha musantawa, yana mai cewa lokacin yakin neman zabe bai yi ba.

Kuma a ko da yaushe shugaban majalisar ta dattawa ya samu damar yin tsokaci a kan dangantakar bangarorin biyu yakan ce babu wani sabani a tsakaninsu, kuma a shirye yake ya yi aiki domin tabbatar da nasarar gwamnatin Buhari, "wacce na yi ruwa da tsaki wajen ganin ta lashe zabe".

Da alama wannan ikirari nasa na da kanshin gaskiya, a cewar Malam Kabiru Sufi Sa'id, na Sashen koyar da kimiyyar siyasa a Kwalejin Share Fagen shiga Jami'a ta Kano kuma mai sharhi a kan harkokin yau da kullum.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zaben da aka yi wa Saraki a matsayin shugaban majalisar dattawan ya kawo baraka

A cewarsa, "Bukola Saraki ya sha ganawa da Shugaba Buhari musamman idan aka samu wani batu da ke bukatar a yi sulhu tsakanin majalisar dokoki da bangaren zartarwa.

'Yan Najeriya ba za su manta da irin hatsaniyar da kasafin kudin shekarar 2016 ya janyo ba kuma duk da kai-komon da aka rika yi a kansa, shugaban majalisar dattawan ya yi uwa da makarbiya wajen ganin an shawo kan wannan matsala. Idan da a ce ba ya goyon bayansa ba zai yi abubuwan da yake yi ba."

"Kar ka manta cewa tun da farko shugaban kasa ne ya yi sake wajen mika komai a hannun jam'iyyar APC shi ya sa Saraki ya bijirewa jam'iyyar," in ji Malam Sufi.

Ya kara da cewa "Da a ce ya yi la'akari da cewa akwai bukatar ya tsaya tsayin daka wurin ganin an zabi shugabannin majalisar dokokin da yake son aiki da su da wasu matsalolin ba za su taso ba."

Haka kuma a lokacin da aka nada ministoci, duk da cewa an yi wa wasu daga cikinsu zargin cin hanci da rashawa, amma 'yan majalisar dattawa ba su yi kasa a gwiwa ba wurin tantance dukkaninsu.

Hakan, a cewar Malam Kabiru Sufi Sa'id, ya nuna cewa 'yan majalisar dattawan na son yin aiki da Shugaba Buhari.

Shi kan sa Bukola Saraki ya shaida wa BBC cewa babu wata matsala tsakaninsa da Shugaba Buhari, yana mai cewa wasu 'yan siyasa ne, wadanda suka kwace ragamar tafiyar da mulkin kasar daga hannun Shugaba Buhari, ke yunkurin shafa masa kashin kaji domin su gusar da kyakkyawar alakar da ke tsakaninsu.

Saraki ya kara da cewa shi kadai ne ya shaida wa duniya cewa Shugaba Buhari na dab da komawa Najeriya daga jinyar da ya yi a birnin London domin hankalin 'yan kasar ya kwanta duk kuwa da cewa mutane da dama sun ziyarci shugaban kasar amma da suka koma gida suka yi gum da bakinsu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Saraki ya ce bita da kullin siyasa ce ta sa aka kai shi kotu

Sai dai batun tabbatar da shugaban riko na hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, Ibrahim Magu, wanda sau biyu majalisar dattawa na yin fatali da shi, ya sake sanya shakku a zukatan 'yan Najeriya a kan sahihancin dangantakarsu da Shugaba Buhari.

'Yan kasar dai na ganin 'yan majalisar dattawan sun ki tabbatar da Magu ne saboda ba sa goyon bayan yakin da Shugaba Buhari ke yi da cin hanci da rashawa, musamman ganin cewa da dama daga cikinsu na gaban kotuna daban-daban domin kare kansu daga zargin da ake yi musu na cin hancin.

Amma Mr Saraki da ma sauran 'yan majalisar sun sha nanata cewa sun dauki matakin ne ta hanyar yin amfani da abin da doka ta ce.

Shi ma Malam Kabiru Sufi Sa'id ya goyi bayan 'yan majalisar a kan wannan batu, inda ya ce: "Ya kamata a rika yi wa 'yan majalisar dattawan adalci. Sun yi amfani da rahoton da hukumar tsaro ta farin kaya, DSS ta tura mus ne, wanda ya zargi Ibrahim Magu da aikata ba daidai ba; don haka idan ma akwai mai laifi a cikin wannan batu, to bangaren zartarwa ne domin su suka zargi shugaban riko na EFCC."

A cewarsa, yana da matukar wahala 'yan Najeriya su daina zargin 'yan majalisar kan kin yin aiki da Shugaba Buhari ganin cewa idanunsu sun rufe kuma "ba sa ganin laifin bangaren zartarwa duk kuwa da cewa akasarin tsamin dangantakar da ke tsakaninsu ya samo asali ne daga fadar shugaban kasa."

Ita dai fadar shugaban kasar, a nata bangaren, ta nace cewa babu wani sabani tsakanin bangarorin biyu, kuma suna ci gaba da aiki tare.

Labarai masu alaka