Iyalan 'yan sanda sun yi zanga-zanga a Faransa

france Hakkin mallakar hoto AFP/getty
Image caption Matan jami'an 'yan sanda da suke cikin fushi yayin da suke zanga-zanga

A Faransa, iyalan jami'ai 'yan sanda sun gudanar da zanga-zanga a Paris, kusa da hasumiyar Eiffel, kwanaki biyu bayan wani dan bindiga ya bude wuta kan wata motar safa, inda ya kashe dan sanda guda.

Masu zanga-zangar sun rika sakin balan-balan zuwa sama, bakake da masu launin hoda, domin yin nuni ga 'yan sandan da aka kashe, da kuma iyalansu da suka bari.

Matar wani dan sanda ce ta kafa kungiyar matan jami'an 'yan sanda da suke cikin fushi a watan Fabrairu, bayan shugaba Francois Hollande ya ziyarci Theo asibiti, wata matshiya bakar fata da wani dan sanda ya ci zarafinta da kulki.

Lamarin wanda 'yan sanda suka ce akasi ne aka samu, ya haifar da zanga-zanga da yin barazana ga 'yan sanda ta shafukan sada zumunta.