Ilimin kimiyya: Dubban mutane sun yi zanga-zanga a duniya

ameria Hakkin mallakar hoto AFP/getty
Image caption Ana gudanar da zanga-zangar ne a birane fiye da dari biyar

Mutane a wasu kasashen duniya sun gudanar da zanga-zanga domin nuna goyon baya ga ilimin kimiyya, a inda dubban daruruwan mutane suka yi tir da abin da suka kira manakisa ta siyasa kan darasin.

An gudanar da babbar zanga-zangar ne a birnin Washington na Amurka, inda daya daga cikin manyan masu ilimin kimiyya na kasar Dr Jonathan Foley, ya ce ana kalubalantar sakamakon bincike-bincike na kare lafiya, da muhalli.

Dr. Foley ya bayyana hakan a matsayin wata karfa-karfa ta siyasa.

Akasarin masu zanga-zangar, suna fushi ne da shugaba Trump na Amurka wanda ya rage kudin gudanar da binciken kimiyya, wanda kuma ya bayyana matsalar sauyin yanayi a matsayin holoko.

Ana gudanar da zanga-zangar ne a birane fiye da dari biyar.