'Yan bindiga sun harbi marubuciya Gallmann a Kenya

kenya Kuki Gallmann Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kuki Gallmann ta shafe fiye da shekaru 40 da komawa Kenya da zama daga Italiya

'Yan bindiga a Kenya sun harbi wata mai fafutukar raya gandun daji da dabbobi, sannan kuma marubuciya, Kuki Gallmann, inda suka raunata ta.

An dauki Kuki Gallmann a jirgin helikofta zuwa asibiti sakamakon harbinta a ciki da a kayi a rukunin gidajenta dake yankin Laikipia.

A watan jiya, wasu da ake zargi makiyaya ne suka kona wani masaukin masu yawon bude ido nata na alfarma.

A 'yan watannin nan, an yi ta samun fadace-fadace, yayin da makiyaya ke kora dabbobinsu cikin gonakin mutane domin kiwo saboda fari da a ke fama da shi.

Gallmann mai shekaru 73, ta koma Kenya ne da zama daga Italiya fiye da shekaru arba'in da suka wuce.

Ta yi fice a duniya saboda littafin da ta rubuta "I Dreamed of Africa" wanda daga baya aka yi fim akan labarin da littafin ya kunsa.