An tuhumi wasu da cin zalun baunaye a India

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mabiya addinin Hindu ba su dauki baunaye a da daraja kamar saniya ba

A kasar India, 'yan sintiri ko 'yan banga kamar yadda ake kiransu a wasu wurare, sun lakada wa wasu mutane uku duka, saboda an same su sun dauko baunaye a mota zuwa mayanka.

Rahotanni sun ce a maimakon 'yan sanda su tuhumi 'yan bangan da bugi mutanen, sai 'yan sandan suka shigar da kara suna zargin mutanen da aka yi wa dukan, da aikata laifin cin zalun baunayen.

Ba kamar yadda a ke daukan shanu a Indiya ba, mabiya addinin Hindu ba su dauki baunaye a matsayin halittu masu tsarki da ba a cin namansu ba.

A farkon wannan watan, wasu da a ke zargi masu fafutukar kare shanu a Rajasthan, suka kashe wani mutun Musulmi, saboda ya dauko saniya a mota.

A na tatsar nonon shanu ne kawai, amma ba a yarda a yanka shanun ba domin cin namansu.

A wancan lokaci, wani minista a gwamnatin kasar ya ce da mutumin da a ka kashe din, da wadanda suka kashe shi, duk suna da laifi.