Kasashen da suka fi kashe wa sojojinsu kudi

Yanzu Rasha ta zarta Saudi Arabia kashe wa sojoji kudi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yanzu Rasha ta zarta Saudi Arabia kashe wa sojoji kudi

Wani sabon bincike ya gano cewa Rasha ita ce kasa ta uku a duniya da tafi kashe wa sojojinta kudi, inda ta zarta Saudi Arabia.

Binciken wanda cibiyar bincike ta Stockholm ta gudanar, ya gano cewa kudin da Rasha ta kashe wa sojojinta a bara ya zarta dala biliyan siitin da tara, duk da raguwar kudaden shigar da ta samu sakamakon faduwar farashin mai da iskar gas a kasuwannin duniya, da ma takunkumin da kasashen yamma su ka kaka ba mata.

Har yanzu dai Amurka ce kasa ta farko da tafi kashe wa sojoji kudade, inda ta ke kashe fiye da dala biliyan dari shida a duk shekara.

China ita ke bin Amurka wajen kashe wa sojoji kudi, inda ta ke kashe musu dala biliyan dari biyu da goma sha biyar.

A bara Saudi Arabia ce ke bin China wajen kashe wa sojoji kudi, amma sai gashi yanzu Rasha ta zarta ta, in da yanzu tazo ta hudu.

Labarai masu alaka