Nigeria: Ban gaji biliyan shida ba- Sarki Sanusi

Sanusi Lamido Sanusi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masarautar Kano ta musanta zarge-zargen facaka da kudin da aka yi wa Sarki Muhammaduy Sanusi na II

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya ce abin da ya gada bai wuce kimanin naira biliyan ɗaya da miliyan 800 ba daga sarkin Kano, marigayi Ado Bayero, sabanin naira biliyan shida da wasu kafofi ke yaɗawa.

A bayanin da ya yi wa manema labarai a ranar Litinin, Ma'ajin Kano wanda shi ne kuma Walin Kano, Alhaji Bashir Wali, ya ce abin da Sarki Sanusi ya gada daga Sarki Ado Bayero shi ne N2,875,163,431.17.

Bayanin na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta fara bincike a kan zargin facaka da kudi da ake yi wa sarkin.

Ma'ajin Kanon ya kara da cewar kafin Sarkin Kano Ado Bayero ya rasu "an fitar da N981, 784,503.73 wanda aka biya kwamitin gina gandun sarki Ado Bayero na Darmanawa domin ci gaba da wannan aikin."

Har ila yau, ma'ajin ya kuma ce "saboda haka abin da ya rage a wannan lokaci bai wuce N1,893,378,927.38 ba. Wannan shi ne abin da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya gada."

Alhaji Bashi Wali ya ci gaba da cewa bayan gadon kudin akwai ayyukan da gwamnatin Rabiu Musa Kwankwanso (tsohon gwamnan Kano) ta ba da izinin gyara wasu gine-gine a cikin gidan sarki bayan wasu wuraren sun rurrushe.'

Ya ce ba a fara aikin ba sai lokacin da sarki Sanusi ya hau karagar mulki, ya kara da cewar gidan ya sauya siffa.

Alhaji Bashir ya ce gaskiya ne masarautar Kano ta biya Dabogate kudi N152, 627,723 inda ya yi bayanin cewar an bayar da kudin ne saboda gyaran fada da kuma sayen kujeru da sauransu saboda mafi yawancin abubuwan da ke fada na tsohon sarkin da ya shafe shekara hamsin yana kan karagar mulki ne.

Ya ce motocin da tsohon sarkin ya bari nasa ne na kashin kansa, kuma bayan rasuwarsa aka yi musu kudi inda masarautar Kano ta biya (miliyan 180) domin su zama mallakarta.

Game da zargin kashe naira miliyan 15 kan tafiye-tafiye, masarautar Kanon ta ce ba haka lamarin yake ba. Ma'ajin Kanon ya ce an kashe kudin kan gyaran zauren da ake fadancin dare a lokacin azumi.

Amman kuma masarautar ta amince cewar an kashe naira miliyan goma sha biyu kan kudin tikitin tafiyar 'yan tawagar sarki, inda ta kara da cewar shi sarkin Kano da kudinsa yake sayen tikitin tafiya da kansa.

Masarautar ta musanta sayen motar kasaita kirar Rolls Royce, da cewa abokan Sarki Sanusin ne suka ba shi kayuta. Sannan dangane da sayen mota mai sulke fadar ta kara da cewa gwamnatin jihar Kano ce ta ba ta umurnin sayen motocin bayan harin da aka kai wa marigayi Ado Bayero.