Ta yaya za a magance zazzabin cizon sauro?

Cutar Malaria ta fi kashe kananan yara a kasashe maso tasowa Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption Cutar Malaria ta fi kashe kananan yara a kasashe maso tasowa

Yayin da a ranar Talata ake bikin ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauro ta duniya, wasu shugabanni a Najeriya sun danganta karuwar matsalar ga dabi'un jama'a na rashin tsaftace muhallan su.

Gwamnan jihar Zamfara Alhaji Abdul'Aziz Yari Abubakar, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, ya ce gwamnatocin kasar ana su bangaren na daukar matakai don magance karuwar zazzabin cizon sauro, sai dai ya ce wajibi ne al'umma sai sun bada gudunmuwa.

Wasu 'yan Najeriyar dai na ganin rashin mayar da hankali daga bangaren shugabanni shi ne ya sa har yanzu aka kasa magance matsalar zazzabin cizon sauro a kasar.

A cewar hukumar lafiya ta Majalisar Dinikin Duniya, wato WHO, daga shekarar 2001 zuwa yanzu, an samu nasarar hana kamuwa da cutar har sau miliyan 663 a yankin nahiyar Afirka kudu da hamadar Sahara, inda a nan ne ake samun kashi 90 cikin 100 na masu kamuwa da cutar.

Ana dai amfani da hanyoyi daban-daban wajen hana kamuwa da cutar, amma kuma wasu daga cikin hanyoyin da ake amfani da su din na da matukar hadari.

A wani labarin kuma, hukumar lafiya ta duniya, ta ce a karon farko za ta fara riga-kafin cutar zazzabin cizon sauro a kasashe uku na Afrika da suka hada da Ghana da Kenya da kuma Malawi.

Hukumar ta bayyana cewa a shekara mai zuwa ne za a fara riga-kafin.

Kimanin jarirai dubu da dari bakwai ne ake sa ran za su amfana da allurar wadda za a kwashei shekaru biyu ana yi.

Kasashen Afrika ne dai suka fi fama da cutar zazzabin cizon sauron, kuma yawancin wadanda ke mutuwa sakamakon kamuwa da ita yara ne.

Labarai masu alaka