Buhari zai rika yin aiki daga gida - Lai Mohammed

Buhari Hakkin mallakar hoto Kaduna state government
Image caption Buhari ya ce bai taba yin jinya irin wacce ya yi a London ba

Hukumomi a Najeriya sun ce Shugaban kasar Muhammadu Buhari zai rika yin aiki daga gidansa da ke fadar gwamnati bayan ya gaza halartar taron majalisar zartarwa karo biyu a jere.

Wannan shi ne karo na biyu da shugaban bai halarci taron majalisar zartarwa ba, abin da ya kara jefa fargaba kan halin da yake ciki.

Sai dai ministan watsa labarai Lai Mohammed, ya ce shugaban zai rika yin aiki daga gidansa, inda za a rika kai masa fayil-fayil da sauran muhimman abubuwan da ke bukatar sanya hannunsa gida.

Ya kara da cewa shugaban ya nemi mataimakinsa da ya jagoranci taron majalisar.

Amma daga bisani Lai Mohammed ya fitar da sanarwar da ke cewa yana nufin ranar Laraba ne kawai zai yi aiki a gidan.

'Yan kasar da dama na ganin shugaban bai halarci taron ba ne saboda rashin lafiyar da yake fama da ita, kuma wasu na nuna damuwa kan halin da yake ciki.

Tun bayan da shugaban na Najeriya ya koma kasar daga jinyar da ya kwashe kusan kwana 50 yana yi a birnin London, ya ce ba zai rika yin aiki sosai ba saboda yanayin jikinsa.

Tun bayan da Shugaba Buhari ya dawo kasar dai, ba kasafai yake bayyana a bainar jama'a ba.

Mataimakinsa Yemi Osinbajo ne yake gudanar da yawancin al'amuran gwamnati, kuma wasu na ganin hakan yana kawo tsaiko wurin tafiyar da al'amura.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yemi Osinbajo ne yake gudanar da yawancin al'amuran gwamnati

Sai dai mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa babu wani abu da ya tsaya a harkar gwamnati saboda matakin da shugaban ya dauka.

"Ya fada da bakinsa cewa bai taba yin jinya wacce ta ba shi wahala kamar wacce ya yi a birnin London ba," kuma ya fada cewa zai ci gaba da huta wa, in ji Garba Shehu.

A lokacin jinyar da ya yi dai, sai da likitoci suka kara masa jini, ko da yake bai fadi larurar da ke damunsa ba.

A lokacin, shugaban na Najeriya ya ce yana samun sauki sosai, "amma watakila nan da makonni kadan masu zuwan zan koma asibiti".

Shugaban dai yakan fito masallaci da ke fadarsa duk ranar Juma'a domin halartar salla.

Labarai masu alaka